Wike ya ƙwace filin Sakatariyar PDP da ke Abuja
Aminiya ta ruwaito cewa filin na Jamiyyar PDP na daga cikin filaye 4,700 da Ministan ya ƙwace a Abuja.

Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ƙwace wani fili mallakar sakatariyar Jam’iyyar PDP da ke Abuja.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun shugaban sashen kula da filaye na Abuja, Chijioke Nwankwoeze.
- Janar Tsiga ya shafe kwanaki 40 a hannun masu garkuwa duk da biyan kuɗin fansa
- Kofin Duniya: ’Yan wasan cikin gida 8 da Super Eagles ta gayyata
Nwankwoeze ya ce an yanke hukuncin ƙwace filin ne sakamakon gazawar babbar jam’iyyar adawar na biyan kudin gini na shekara shekara.
Wasiƙar ta ce PDP ta gaza biyan kuɗin tun daga ranar 1 ga watan Janairun 2006 zuwa 1 ga watan Janairun 2025, duk da sanarwar da hukumar gudanarwar babban birni (FCTA) ta wallafa a jaridu da dama tun daga shekarar 2023 kan buƙatar biyan kuɗaɗen.
“Saboda haka ana sanar da cewa a yanzu filin mai lamba 243 da ke tsakiyar birnin Abuja, Cadastral Zone A00, ya zama mallakin Hukumar Gudanarwar Babban Birnin.”
Aminiya ta ruwaito cewa filin na Jamiyyar PDP na daga cikin filaye 4,700 da Ministan ya ƙwace a Abuja.