Wike ya hana Atiku wurin taron yakin neman zabe a Ribas

Yanzu haka dai ana jira a ga inda gwamnonin G5 da Wike yake jagoranci za su karkata da kuma irin abin da zai biyo baya.

Wike ya hana Atiku wurin taron yakin neman zabe a Ribas

Nyesom Wike

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya soke izinin taron yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da za a gudanar ranar 11 ga watan Fabrairu da muke ciki.

Sanarwar da Gwamnatin Jihar Ribas ta fitar ta soke izinin da ta bayar na yin taron a filin wasa na Adokiye Amiesimaka da ke Fatakwal, bisa zargin Atiku da hada baki da dan takarar gwamnan jihar na Jam’iyyar APC, Tonye Patrick Cole.

Wasikar da ke dauke da sa hannun Kwamishinan Wasanni na Jihar Ribas, Christopher Green, ta zargi APC da yin kaurin suna a jihar wajen “fadace-fadace, kashe-kashe, harbe-harbe da kuma tayar da abubuwan fashewa,” a tarukanta da suka gabata.

“Don haka, Gwamnatin Jihar Ribas ba za ta iya gangancin da zai ba da dama a lalata kadarorin da ta kashe makudan kudaden talakawa a kansu ba,” in ji shi.

Wannan na zuwa ne a yayin da ake ci gaba zaman doya da manya tsakanin Atiku Abubakar da bangaren Gwamna Wike, da ke jagorantar takwarorinsa biyar na Jam’iyyar PDP (G5).

Gwamnonin G5 sun juya wa Atiku baya, kuma ana zargin za su yi masa kafar ungulu a kan hadafinsa na zama shugaban kasa, wanda karo na biyar ke nan yana nema.

Sai dai kuma, bangarensa ya yi kurarin cewa ko babu su Wike zai ci zabe.

Wannan takun saka dai ta samo asali ne bayan zaben fidda gwanin PDP da Atiku ya lashe, Wike ya zo na biyu.

Wike wanda ya yi zargin an ci amanarsa a zaben ya so zama abokin takarar Atiku, kamar yadda kwamitin wasu masu ruwa da tsaki da dan takarar ya kafa suka ba da shawara, amma Atiku ya yi watsi da hakan, ya dauki Gwamnan Delta, David Umahi, lamarin da ya kara harzuka Wike da magoya bayansa.

A bangare guda kuma, Wike da G5 sun shardanta wa Atiku sauke shugaban PDP na Kasa, Iyorchia Ayu, wanda suke zargi da magudi da saba tsarin zaben fidda dan takarar da kuma kasancewarsa daga Arewa, yankin da Atiku ya fito.

Amma dan takarar ya ki amincewa, inda ya ce hakan ba za ta yiwu ba, sai bayan sun ci zabe.

Duk kokarin Atiku na lallashin G5 ya gagara, inda suka ja layi, a karshe suka sanar cewa a watan Fabrairu da muke ciki za su bayyana dan takarar da za su goyi baya a zaben shugaban kasa da ke tafe ranar 25 ga wata.

Yanzu haka dai ana jira a ji inda gwamnonin G5 da Wike yake jagoranci za su karkata da kuma irin abin da zai biyo baya.