Wike ya haramta haya da motoci marasa fenti a Abuja

Direbobin Uber ma dole su yi rajista da hukumomin tsaro

Wike ya haramta haya da motoci marasa fenti a Abuja

Tsohuwar ajiya (NAN)

Ministan Birnin Taraya, Nyesom Wike, ya ce nan ba da da jimawa za a haramta wa maohtocin haya marasa fantin gwamnati aiki a birnin.

Wike ya shaida wa wani taron ’yan jarida a Abuja cewa yin hakan ya zama dole domin kawar da ayyukan masu motocin da ke yi wa fasinoji fashi, wadanda aka fi sani da ’yan ‘One Chance’ a birnin.

A cewarsa, duk da cewa ayyukan ’yan ‘One Chance’ sun ragu saosai, akwai bukatar daukar tsaruraran matakai domin kawo karshensu.

“Ba za mu bar motocin hayara marasa rajista da kuma fentin da aka kayyade musu su yi aiki a Abuja ba.

“Da haka ne za a iya tantance direbobin duk motocin da ke haya a Abuja a kan kai’ida da kuma kare rayuwar al’umma daga fadawa a hannun bata-gari,” in ji shi.

Ministan ya kuma bayyana cewa direbon haya na kamfani irin su Uber da dangoginsu ma, dole su yi rajista da hukuma domin a tantance a san ko su waye.

“Haka zalilka jami’an tsaro za su yi musu rajista kuma su dauki bayananansu, saboda idan kara zube za a yi abubwa dole za a samu matsaloli,” in ji Wike.

Haka kuma ya koka game da rashin tashohoin motocin haya da ke zirga-zirga a garin Abuja, amma ya ce za a fara gina guda uku a bana, daga bisani a kara wasu.

Da haka ne a cewarsa mazauna da hukumomi za su san motocin da kowa ya hau, ko da wani abu ya faru.