Ministan Abuja ya haramta tallace-tallace

Wike ya zargi masu tallar da kasa kaya a gefen titi da hannu wajen taɓarɓarewar tsaro a Abuja

Ministan Abuja ya haramta tallace-tallace

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya haramta tallace-tallace da kuma saye da sayarwa a gefen titunan birnin Abuja.

Wike ya bayyana cewa ya yi amanna cewa masu tallace-tallace da masu kasa kaya a gefen tituna na ba da gudunmawa wajen taɓarɓarewar tsaro da kuma aikata miyagun laifuka a Abuja.

Don haka ya ce, “Dole mu kawar da masu tallace-tallace daga titunan,” saboda yadda suke kawo ƙazanta da kuma taimakawa wajen taɓarɓarewar tsaro.

Da yake jawabi ga manyan jami’an kula da kuma bunƙasa birnin, Wike ya kuma umarce su da su kawo ƙarshen yadda mutane ke ajiye motoci barkatai a birnin nan ba da jimawa ba.

Sannan ya hore su da su yi abin da ya dace wajen dawo da martabar Abuja a matsayinta babban birnin tarayya kuma fadar gwamnati.

“Abu mafi muhimmanci shi ne, dole ne mu  tabbatar da cewa, Abuja ta dawo da martabarta kuma yadda aka tsara ta tun asali.

“Na kuma kewaya sassan Abuja, kuma na gano cewa, akwai duhun rashin wutar lantarki a wurare masu yawa.

“Saboda haka, abin da za mu yi shi ne, tabbatar da samuwar wutar lantarki nan ba da jimawa ba,” in ji Wike.

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano