Wilberforce Juta: Jihar Adamawa na zaman makoki
Jihar Adamawa ta fara zaman makoki na kwana uku bayan rasuwar tsohon Gwamnan Tsohuwar Jihar Gongola, Ambasada Wilberforce Bafte Juta. Gwamna Umaru Fintiri yayin juyayin rasuwar jigon a jam’iyyar PDP, ya yaba da kyawawan ayyukan mamacin wajen bunkasa rayuwa da ci gaban siyasa, wanda ya ce za a dade ana yabawa. “Domin girmama dattijon, Gwamna Ahmadu […]
Jihar Adamawa ta fara zaman makoki na kwana uku bayan rasuwar tsohon Gwamnan Tsohuwar Jihar Gongola, Ambasada Wilberforce Bafte Juta.
Gwamna Umaru Fintiri yayin juyayin rasuwar jigon a jam’iyyar PDP, ya yaba da kyawawan ayyukan mamacin wajen bunkasa rayuwa da ci gaban siyasa, wanda ya ce za a dade ana yabawa.
“Domin girmama dattijon, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya ayyana zaman makoki na kwana uku daga Asabar 15 ga Agusta, 2020”, inji sanarwar da kakakin gwamnan, Humwashi Wonosikou ya fitar.
Marigayi Juta wanda shi ne gwamnan tsohuwar Jibar Gongola a 1983, ya kuma yi Jakadan Najeriya a Zimbabwe daga shekarar 2000 zuwa 2004.