Winie Mandela: Uwar kasa ’yar fafutika ta rasu

Tarihi ba zai manta da tsohuwar matar marigayi Nelson Mandela, Winnie ba wadda ta rasu tana da shekara 81 a ranar Litinin da ta gabata. Winnie Madikizela Mandela ta kasance kan gaba wajen yaki da nuna wariyar launin fata a kasar Afirka ta Kudu. Marigayiyar tana daga cikin mutanen da suka yi wa tsohon Shugaba […]

Winie Mandela: Uwar kasa ’yar fafutika ta rasu

Tarihi ba zai manta da tsohuwar matar marigayi Nelson Mandela, Winnie ba wadda ta rasu tana da shekara 81 a ranar Litinin da ta gabata.

Winnie Madikizela Mandela ta kasance kan gaba wajen yaki da nuna wariyar launin fata a kasar Afirka ta Kudu.

Marigayiyar tana daga cikin mutanen da suka yi wa tsohon Shugaba Mandela rakiya yayin da aka sallame shi daga gidan yari – bayan ya kwashe fiye da shekara 27 yana tsare.

Mai magana da yawun iyalanta bictor Dlamini ya ce: “Ta rasu ne bayan ta yi fama fa doguwar jinya a safiyar ranar Litinin,” kamar yadda BBC ta ruwaito.

An haifi marigayiyar ce a 1936 a Lardin Eastern Cape wanda a da ake kira Transkei.

Ta fara haduwa da Mandela a shekarun 1950 kuma sun kwashe shekara 38 a matsayin ma’aurata – koda yake kimanin shekara 30 ba sa tare da juna saboda Mandela yana gidan yari.

Duk da cewa aurensu ya mutu a 1996, Winnie ta ci gaba da amfani da sunan Mandela da kuma hulda da shi.

Bayan da aka tsare Mista Mandela, Madikizela-Mandela ta karbi ragamar fafutikar kwato ’yancin bakaken fata a kasar Afirka ta Kudu daga inda Mandela ya tsaya. Ita ma an sha daure ta saboda wannan gwagwarmayar da ta yi ta neman kafa adalci da samun ’yanci.

Ga magoya bayanta, ta kasance ‘Uwar kasa’ saboda soyayyar da suke da ita a gare ta.