Wizkid da Tems sun lashe lambar yabo ta AMA a Amurka

Kyautar AMA dai ita ce mafi girma a duniya wadda magoya baya ke zaben tauraronsu.

Wizkid da Tems sun lashe lambar yabo ta AMA a Amurka

Wizkid da Tems

Fitaccen mawakin Najeriya da ya shahara a salon wakar Afrobeat, Ayodeji Ibrahim Balogun da aka fi sani da Wizkid ya lashe lambar yabo ta AMA a Amurka.

Haka kuma takwararsa, Temilade Opaniyi da aka fi sani da Tems, ita ma ta sake daga martabar kasar a idon duniya a bikin bayar da lambar yabo ta AMA a Amurkan.

Wikzid ya kafa tarihi bayan ya doke Burna Boy da Ckay da Tems da Fireboy, inda ya zama mutun na farko da ya lashe kyautar a bangaren mawakan Afrobeat a bana.

Tems ta yi nasara ce bayan an zabe ta a matsayin wadda ta fi nuna hakaza a bana a bangaren salon wakar R&B.

A karon farko kenan da Wizkid ke lashe wannan kyauta bayan da sau uku yana takarar lashe ta amma bai samu nasara ba, sai a bana.

A karo na 50 kenan da ake gudanar da bikin na AMA wanda aka gudanar a dakin taro na Microsoft Theatre da ke Los Angeles a Amurka a ranar Lahadi wanda sharararren mai gabatar da shirin talabijin Wayne Brady ya jagoranta.

Kyautar AMA dai ita ce mafi girma a duniya wadda magoya baya ke zaben tauraronsu.