Wurare 10 mafiya hatsari a Abuja

Wadannan wurare sun yi kaurin suna wajen aikata miyagun laifuka.

Wurare 10 mafiya hatsari a Abuja

Matsalar tsaro na daya daga cikin manyan abubuwan da ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya tsawon shekaru, lamarin da ke ci gaba da kawo cikas ga tattalin arziki da kuma rayuwar yau da kullum.

Bayan ga ta’addanci, garkuwa da mutane, hare-hare da ake yi wa mutane yau da kullum a wasu sassan Najeriya, birnin tarayya Abuja, bai tsira ba, saboda akwai wasu wurare da suka yi kaurin suna wajen aikata miyagun laifuka.

Binciken Aminiya, ya gano wasu gawurtattun wurare da suka yi fice wajen aikata miyagun laifuka a babban birnin tarayya.

Kididdigar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ksa ta nuna cewa, shataletale Julius Berger, Gundumar Maitama, Mabushi, Shataletalen Apo, Area 1 da Area 3, Galadimawa, hanyar Fiiln Jirgin Saman Abuja da unguwar Wuse 2, na daga cikin wurare mafiya hatsari a Abuja.

Binciken ya gano yadda bata-gari ke yin basaja a matsayin direbobin motocin haya, suke yi wa mutane kwace, fashi ko damfara.

Kazalika, hukumomi sun gano yadda wadannan bata-garin ke amfani da kango, gine-gine, karkashin gada, kasuwanni, a matsayin maboyarsu.

Gine-gine da ba a kammala ba sun zama wuraren boye mutane da aka sace da kuma aikata muggan laifuka.

Wadannan wuraren na kasa sun yi kaurin suna wajen aikata manyan laifuka a Abuja:

  1. Shataletalen Apo
  2. Titin zuwa filin jirgin saman Abuja (Airport Road)
  3. Shataletalen Area 1
  4. Area 3
  5. Shataletalen Julis Berger
  6. Mpape
  7. Durumi
  8. Galadimawa
  9. Wuse 2
  10. Dei-Dei