Wurare 18 da ke fuskantar barazanar dokar kulle a Najeriya
Kananan hukumomi 18 a Najeriya na fuskantar barazanar dokar kulle kasancewarsu dauke da kaso 60 cikin 100 na masu COVID-19 a kasar. Shugaban Kwamitin Yaki da annobar coronavirus na Fadar Shugaban Kasa Boss Mustapha, bayan gabatar wa Shugaba Buhari rahoton kwamitin a ranar Litinin 29 ga watam Yuni, ya nuna bukatar dokar kulle a kananan […]
Kananan hukumomi 18 a Najeriya na fuskantar barazanar dokar kulle kasancewarsu dauke da kaso 60 cikin 100 na masu COVID-19 a kasar.
Shugaban Kwamitin Yaki da annobar coronavirus na Fadar Shugaban Kasa Boss Mustapha, bayan gabatar wa Shugaba Buhari rahoton kwamitin a ranar Litinin 29 ga watam Yuni, ya nuna bukatar dokar kulle a kananan hukumomim domin dakile yaduwar cutar.
- An bude makarantu da tafiye-tafiye tsakanin jihohi
- Bude makarantu: Sai an kara matakan kariya —Malamai
- Ba mu da shirin sake bude makarantu yanzu – Gwamnatin Kano
“Matakin kulle a kananan hukumomin 18 ba hurumin Gwamnatin Tarayya ba ne, hurumi ne na gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi”, inji shi.
Ko da yake Boss Mustapha bai ambaci sunayen kananan hukomomin ba, wani binciken da Aminiya ta yi na alkaluman da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta fitar zuwa ranar sun jerin kananan hukumomi 20 da suka fi yawan masu cutar.
A cikin kananan hukumomin 20 jihar Legas na kan gaba da 11, inda karamar hukumar Lagos Mainland ke da kaso mafi yawa na masu cutar, su 1,274.
Jihar Legas
- Lagos Mainland (1,274),
- Mushin (458),
- Eti-Osa (403),
- Alimosho (239),
- Kosofe (175),
- Ikeja (168),
- Oshodi/Isolo (132),
- Apapa (131),
- Amuwo Odofin (129),
- Lagos Island (111)
- Surulere (110).
Babban Birnin Tarayya (Abuja)
- (AMAC (536).
Jihar Kano
- Tarauni (248),
- Nassarawa (152).
Jihar Katsina
- Katsina (242).
Jihar Borno
- Maiduguri (167).
Jihar Jigawa
- Dutse (170).
Jihar Ondo
- Oredo (126).
Jihar Bauchi
- Bauchi (114).
Jihar Ogun
- Ado Odo/Ota (107).