Wuraren ibada za su ci gaba da kasancewa a rufe a Abuja
Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Muhammad Musa Bello, ya ce wuraren ibada a yankin za su ci gaba da kasancewa a rufe bisa shawarwarin da kwararru suka bayar da ma Kwamitin Shugaban Kasa a Kan Yaki da COVID-19. Masallatai da majami’u sun kasance a rufe a birnin tsawon watanni biyu a kokarin da ake yi […]
Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Muhammad Musa Bello, ya ce wuraren ibada a yankin za su ci gaba da kasancewa a rufe bisa shawarwarin da kwararru suka bayar da ma Kwamitin Shugaban Kasa a Kan Yaki da COVID-19.
Masallatai da majami’u sun kasance a rufe a birnin tsawon watanni biyu a kokarin da ake yi na dakile yaduwar cutar ta coronavirus.
Ministan, wanda ya yi taro da wakilan mabiya addinan Musulunci da Kirista, a karkashin jagorancin shugaban CAN na birnin tarayya Dokta Samson Jonah da shugaban Kungiyar Limaman Abuja Dokta Tajudeen Bello Adigun, ya bayyana cewa kwararru a bangaren kiwon lafiya da kuma kwamitin dakile yaduwar cutar kasa sun ba da umarnin tsawaita dokar kariya da aka sanya da mako biyu.
- Dage dokar zaman gida: Kare kai na yi wa mazauna Abuja wahala
- Yadda jama’a ke tururuwar fita a Abuja da Legas
Wata sanarwa da mai taimaka masa a kan harkokin yada labarai, Anthony Ogunleye, ya fitar ta ambato ministan yana cewa, “Bisa shawarwari da kuma tattaunawa da kwararru, kwamitin dakile yaduwar cutar ya bukaci a tsawaita matakan da aka dauka makon da ya wuce da wasu karin mako biyu saboda hakan zai bai wa hukumomi da ma daidaikun jama’a damar shiri domin bude dokar kulle da aka sanya”.
Bello ya ce taron da aka yi ya fahimci muhimmancin da shuwagabanni suke bayarwa a kan kare rayuka daga salwanta wanda hakan ya danganci hankali a kan rahoton hukumomin kiwon lafiya da ke nuna cewa nasarar da ake samu ba ta taka kara ta karya ba.
Ministan ya jaddada muhimmancin amfani da kyallen rufe fuska inda ya yi nuni da cewa wanke hannu da kuma ba da tazara za su zama dole idan za a bude wuraren ibadar.
Aminiya ta gano cewa an gudanar da taron ne saboda bukatar da shuwagabannin addinin suka gabatar na bude wuraren ibada sakamakon matsin lamba daga magoya bayansu.