Wurin jiran bas mai intanet da wurin shan shayi kyauta a Dubai
An yi wurin jira bas na zamani a masarautar Dubai da ke cikin Hadaddiyar Daular Larabawa. Wannan sabon wurin jiran bas na dauke da wurin kulla alakar intanet na ‘WI-Fi,’ kyauta da kuma kofin gahawa kyauta.Hukumar sufuri ta masarautar ta bayyana aniyarta ta kafa irin wdannan wuraren jiran bas na zamni har guda 100, masu […]
An yi wurin jira bas na zamani a masarautar Dubai da ke cikin Hadaddiyar Daular Larabawa. Wannan sabon wurin jiran bas na dauke da wurin kulla alakar intanet na ‘WI-Fi,’ kyauta da kuma kofin gahawa kyauta.
Hukumar sufuri ta masarautar ta bayyana aniyarta ta kafa irin wdannan wuraren jiran bas na zamni har guda 100, masu dauke da likon intanet da wurin cajin waya da kuma dan karamin wurin shan shayi da gahawa duk a kyauta.
Sai dai hukumar ta yi nuni da cewa, likon intanet din za a kayyade masa wa’adin da za a bai wa mutum ya yi amfani da shi, don gudun kada wasu su banzatar da abin.
“Ba mu yanke wa’adin lokaci ba, amma za a kayyade gwargwadon lokacin da mutum zai shafe yana jira a wurin jiran bas,” a cewar Mohammad al-Ali jami’in hukumar sufurin masarautar. Kuma an bayyana cewa wadannan wuraren jiran bas-bas din za su fara aiki nan da karshen Janairun shekara mai zuwa. Sannan mafi yawan wuraren jiran an samun yawan al’umma ne.
Tuni dai wannan hukumar ta sufuri (RTA) ke kokarin hana mutane amfani da kananan motoci, don rage yawan cunkoson ababen hawa a hanyoyin dubai.
A shekarar 2014, har kyaututtukan da suka hada da zinare aka rika bai wa mutanen da suka yi amfani da motocin sufuri na hukuma. Labarin wadannan wuraren jiran bas na zamani da aka kafa a Dubai sun bazu a shafukan BBC da Gulfnews.