Wurin sayar da abinci na yaki da rabuwar aure a kasar Sin
Wata maciyar abincin sayarwa da ke garin Chenglu a kasar Sin ta fara yaki da sakin aure da ke karuwa. Wannan maciyar abinci dai ta saba gudanar da bukukuwan aure, inda anguna da amare ke musayar zobban aure, tare da kudurar aniyar kasancewa tare da juna har abada.Matakin da maciyar abincin ta dauka shi ne, […]
Wata maciyar abincin sayarwa da ke garin Chenglu a kasar Sin ta fara yaki da sakin aure da ke karuwa. Wannan maciyar abinci dai ta saba gudanar da bukukuwan aure, inda anguna da amare ke musayar zobban aure, tare da kudurar aniyar kasancewa tare da juna har abada.
Matakin da maciyar abincin ta dauka shi ne, duk wadanda za su gudanar da bikin aure a wurin, to dole sai sun tsare ba za su rabu ba, sannan a bukaci su rattaba hannu a kan alkawarin a gaban bakin da suka halarci bikinsu.
Wannan bukata da maciyar abinci ke bijiro wa ma’aurata, ta sanya wasu na ganin cin fuska ne ma a ce an ambaci ‘saki,’ ballantana ma a cusa shi cikin rukunin hada-hadar ranar biki, amma duk da haka sukan sanya hannu. Shi kuwa manajan maciyar abincin sayarwar, cewa ya yi, ana bukatar daukar irin wannan alkawari.
A kasar Sin, alkaluman kididdiga na shekarar 2014 sun tabbatar da karuwar yawan rabuwar aure da kashi 2.6 cikin 100, in an kwatanta da kashi daya da rabi cikin 100 da aka samu a shekarar 2007, kamar yadda sashen kidddiga da tattara bayanai kan zamantakewa ya fitar, a karkashin Ma’aikatar kula da al’amuran al’umma.
Tun bayan da labarin wannan maciya ya bazu a shafukan intanet, dukkan masu mu’amala da shafukan suka yi ta sharhi, inda wani ya rubuto cewa: “rattaba hannu a kan yarjejeniyar ba ta da tasiri. Shin manajan zai bi kadin ma’auratan ne ya tabbatar nan gaba ba za su rabu ba?”
“Kafin a bukaci ma’aurata su rattaba hannu kan yarjejeniyar alkawarin, lallai manajan ya tabbatar da cewa, harkokin kasuwancin wurin sayar da abincin ba zai durkushe ba,” a cewar wani mai lakabin Eleben.
“Wannan maciyar abinci ta yi daidai. Don ko ba komai maciyar ta damu da halin da ma’aurata za su kasance,” a cewar Yueshi, wani mai goyon bayan shirin maciyar sayar da abincin.