Wutar Kaikayi: Nazarin littafin Tarkon Mut’a

Sunan Littafi: Tarkon Mut’a (Wasan Kwaikwayo) Sunan Marubuci: Bashir Yahuza Malumfashi Shekarar Wallafa: 2019 Kamfanin Wallafa: Gizago Publishing Enterprises Yawan Shafuka: 100 Lambar ISBN: 978-2149-99-3 Farashi: Naira 500 Gabatarwa: Littafin Tarkon Mut’a, wani sabon littafin wasan kwaikwayo ne da ya bayyana a farkon wannan shekarar Masihiyya ta 2019, don cike wani bangare na babban gibin […]

Wutar Kaikayi: Nazarin littafin Tarkon Mut’a

A hagu, Shaikh (Dokta) Muhammad Mansur Ibrahim Sakkwato, yana amsar kwafin littafin Tarkon Mut’a daga hannun Malam Hussani Kabir ‘Yar’aduwa

Sunan Littafi: Tarkon Mut’a (Wasan Kwaikwayo)

Sunan Marubuci: Bashir Yahuza Malumfashi

Shekarar Wallafa: 2019

Kamfanin Wallafa: Gizago Publishing Enterprises

Yawan Shafuka: 100

Lambar ISBN: 978-2149-99-3

Farashi: Naira 500

Gabatarwa:

Littafin Tarkon Mut’a, wani sabon littafin wasan kwaikwayo ne da ya bayyana a farkon wannan shekarar Masihiyya ta 2019, don cike wani bangare na babban gibin da ke akwai tsakanin rubutaccen wasan kwaikwayo da sauran ’yan uwansa a fannin rubutaccen adabi, wato waka da rubutun zube. Babu shakka kuwa wannan yunkuri abin yi wa maraba ne, tare da gode wa kokarin marubucin na samar da wannan littafi a dai dai wannan lokaci.

Marubucin littafin kuwa, Malam Bashir Yahuza Malumfashi, fasihin marubuci ne, musamman a fannin rubutattun wakokin Hausa da na Turanci, baya ga kasancewarsa zakakurin dan jarida. Hakika fitowar wannan littafi daga gare shi ba zai zama abin mamaki ba, duk da kasancewar ba fannin da aka fi sanin sa da shi ba ne.

Jin dadin samun nusuhar littafin ta sa har na rubuta wasu ’yan baitocin yabawa, wanda a cikinsu na kuduri aniyar idan na karance zan yi kokarin rubuta wani dan sharhin adabi kan littafin, kasancewar wasu sun rigaye ni wajen rubuta sharhin kunshiyar littafin, duk da kasancewata karamin almajiri kan wannan fanni.

Tsarin Littafin:

Marubucin ya karkasa labarin zuwa sassa (Fitowa) 13. Kowace fitowa kuma an karkasa ta zuwa kananan sassa (Shiga) kamar yadda ya kira tsarin, don saukaka warwaren zaren labarin.

Yadda aka tsara labarin ya yi armashi sosai, inda aka fara da kawo wata matsala, sannan aka shiga warwarar ta sannu a hankali har zuwa karshen littafin.

Abu guda marubucin ya manta, shi ne gabatar da sunayen ’yan wasa da matsayin kowanne a cikin wasan, kamar yadda galibin marubuta littafan wasan kwaikwayo sukan yi, don taimaka wa mai karatu wajen sanin adadin ’yan wasan yayin gabatar da shi a aiwace da fahimtar matsayin kowane dan wasa tun da farko, ba sai yayin da ya yi nisa a karatu ba.

Jigo da Warwararsa:

Jigon wannan littafi shi ne fadakarwa kan hadarin da ke tattare da akidar Shi’a da ta iso Najeriya kimanin shekaru 30 da suka gabata, wadda guguwarta ke kwasar matasa maza da mata, musamman ta fannin auren wucin-gadi da mabiya akidar suka halatta, wanda ke haifar da sakamakon da kan zamo da-na-sani ga mafi yawan matasa, musamman matan da akan yi amfani da su, daga karshe a bar su da alakakai.

Marubucin ya fara da kawo wani kulli ne, inda matashiya Nana ta wayi gari da bayyanar alamun shigar ciki tare da ita, al’amarin da ta yi kokarin boye shi ga mahaifiyarta amma da yake ciwon ’ya mace na mace ne kamar yadda sukan ce, sai da ta gane, sai dai ba ta nuna ba:

“Likitoci sun ce a daina wasa da laulayin amai da gudawa, a je asibiti da wuri.” (shafi na 3).

A wannan lokacin ne Nana ta farka daga dogon suman gafalar da ta shiga, wanda ya sa har ta saki jiki Dandangi ya hilace ta har ta shiga akidarsa, inda ya yi amfani da wannan dama wajen kulla auren Mut’a da ita, al’amarin da ya haifar da shigar cikin da ta wayi gari da shi.

“Ke kanki yanzu da kika zama ’yar uwa ai kin ga rayuwarki ta sha bamban da ta sauran kawayenki. Kin ga yanzu kin zama masoyiyar Ahlul Baiti ta gaske. Amma da kin murkushe kanki cikin jahilci da bibiyar wata bahaguwar hanya wai ita Sunna!” (Shafi na 7).

Marubucin ya sanya muhimman sakonnin littafin a bakin wasu mutane, musamman Liman da amarya Zahra’u, kamar inda Liman ke cewa:

“Yanzu ko a hankalce, shin mene ne bambancin Auren Wucin-gadi (Mut’a) da karuwanci ko dadiro? Mai dadiro zai nemi karuwa, ya ajiye ta, shi ne abincinta da suturarta da kudin hayarta, amma babu wanda ya daura musu aure… Haka shi ma Auren Mut’a yake, babu waliyyi, babu shaidu, daga kai sai ita za ku kulla shirinku: awa daya, kwana daya, wata daya ko shekara daya…” (shafi na 11).

’Yar wan mahaifin Nana ma, wato amarya Zahra’u ta kusa fadawa irin komar da Nana ta fada, sai dai ita ba auren Mut’a ta yi ba, cikakken aure ta yi irin wanda suke kira da’imi, amma cikin rashin sanin akidar angon nata Dangwaggo. Bayan an yi auren ne ya fito mata da ainihin akidarsa, tare kokarin dulmiyar da ita. Har mata ya rika kai wa gidan ya yi kwanaki da su a matsayin auren Mut’a. Ya kuma nemi ya rika tarawa da ita ta baya (luwadi). Har wani abokinsa ya taba kai mata don ya kwana da ita, shi kuma zai je gidan wancan ya kwana da matarsa, abin da suke kira da Aron farji! Sai dai Allah Ya sa ita a farke take, kasancewar ta san irin wannan akida da kyau. Don haka ta bijire masa fafur, ta goge su sarai shi da malaminsa Malam Dutsimmiy da ya gayyato don ya shawo masa kanta. Ta kafe su da kwararan hujjoji wadanda har suka rasa bakin magana, kamar inda ta ce:

“Ina so ku gane cewa ku ’yan Shi’a karya kuke, karyarku ma karya take game da abin da kuke dangantawa ga Ahlul baiti. Allah (SAW) ya gama bayyana mana ingancin Sahabban ManzonSa tun a littattafan da suka gabaci Alkur’ani…” (shafi na 35).

Hankalin Nana ya kara tashi matuka yayin da ta je dakin Dandangi don shaida masa halin da take ciki, inda ta fara yin arba da wata rigar nono yashe bisa katifarsa, alamar ya kai mace dakin. Nan suka hau rimin gafiya suka fado a na bera, daga karshe dai ya rarrashe ta har fushinta ya dan lafa.

“Lallai na yarda da maganar Hausawa da suka ce fahimta fuska. Shin wai kin mance da ka’idojin addininmu a kan wannan lamari? Ina tunaninki ya shiga ne? Yanzu ke idan na ga kina Mut’a da wani sai in sanya miki kahon zuka?” (shafi na 42).

Daga karshe dai ta shaida masa cikin da take dauke da shi, inda ya nemi su zubar da shi, amma atafau ta ce ba ta yarda ba.

“Kai da kanka ka san cewa na gaya maka ban taba sanin wani da namiji ba face kai. Kuma wallahi ni ba wani abu ya dauke ni har na yarda da Mut’a ba face kaunar ka. Amma dai muddin ka nuna mani butulci, wallahi, wallahi ba za ka ji da dadi ba!” (shafi na 44).

Nana ta koma gida cike da takaici. Ta tuno yadda tun farkon haduwarta da Dandangi wata kawarta Amira a makaranta ta gargade ta game da shi:

“Shi mutumin naki ba bako ba ne ga matan makarantar nan, domin kuwa ya yi nema da wasu da dama daga cikinsu. Kurarsa ta yi kuka a nan Poly ta fannin yadda yake yaudarar mata. A makarantarsu FCE Katsina, babu yarinyar da za ta yarda ya tunkare ta da batun soyayya. Shi ya sa yake zagayowa nan yana samun sabbin dalibai irinki yana hilacewa.” (shafi na 47-48).

Amma wanda ya yi nisa ba ya jin kira. Kasancewar Nana ta gama kamuwa da son Dandangi, sai ta yi wa nasihar kawar tata kunnen uwar shegu, tare da zargin tana yi mata bakin ciki ne ganin ta samu sangalin saurayi. Daga karshe ma ta gargade ta da kada ta sake shiga sha’aninta da Dandangi.

“Gaskiya muddin dai batun Dandangi ne, to ki shafa mani lafiya; iya gani iya kyalewa. Lallai ne ba na son ki kara tsoma mani baki a hidimata da shi, idan ba haka ba kuwa, za ki gamu da bacin ran da ba ki taba gani ba. Haka nan kawai sai mutane su zama Sa’idawa? Ke ba ki san cewa shan koko daukar wa rai ne ba? To ni dai na gaya maki, na dauki Dandangi na saka shi a raina, duk mai bakin ciki sai dai ya mutu Ehee!” (shafi na 49-50).

Nana ta ziyarci ’yar uwarta Amarya Zahra’u, inda ta fada mata halin da take ciki, da matakin da Dandangi ya ba ta shawarar su dauka, wato su zubar da cikin. Bayan tausayawa da taya ta jin takaicin abin, ta ba ta shawarar kada ta kuskura ta zubar da cikin. Ta yi alkawarin idan ta je gidan su Nana ita za ta fada wa mahaifiyarta game da batun:

“Sam! Kada ki fara wannan wautar, domin gaskya bai dace ki dauki wannan karkataccen matakin ba. Ki tuna fa cewa da asara gara gidadanci. Zubar da ciki yana da nasa matsalolin. Kada fa garin neman kiba a samo rama, garin gyaran gira ana iya rasa idon gaba daya! Hanyar lafiya a bi ta da shekara, kuma bai kamata mutum ya yi kuskure biyu a lokaci guda ba.” (shafi na 55).

Nana ta koma gida, ta kulle kanta cikin daki ta shiga tunani. Ita dai tana son ganin ta rabu da cikin da take dauke da shi, amma kuma ga Zahra’u ta hana ta, har ma ta ce za ta fada wa mahaifiyarta. Tana cikin wannan sakar zuci ne Dandangi ya kira ta, ya nemi su hadu kashegari a Katsina don zuwa a zubar da cikin, ya ce sun gama maganar da likitan da zai yi aikin har ma ya biya shi.

“Na riga na biya likitan da zai cire miki cikin nan a Katsina. Don haka gobe tun da safe kada ki ci komai, ki shigo mota ki zo nan Katsina ki same ni. Likitan ya yi mani alkawarin zai cire shi cikin kankanen lokaci, kuma ki dawo gida ba tare da wani ya san ma me kike ciki ba.” (shafi na 58).

Jin wannan tabbaci daga Dandangi, sai lamarin ya sake cude mata, amma ba ta da burin da ya wuce ganin ta rabu da cikin da take dauke da shi, don haka ta kuduri aniyar zuwa Katsinan don haduwa da Dandangi su je a zubar da shi. Sai ta kira Zahra’u, ta yi mata karyar cewa an aiko mata ana neman su a makaranta don karbar sakamakon jarrabawarsu. Ta bukace ta da ta janye batun fada wa mahaifiyarta idan ta zo.

“…Kawai dai ina ganin lokacin sanar da su bai yi ba. Hasali ma, an aiko mani daga Katsina cewa ana neman mu a makaranta… shi ya sa ban so labarin cikin nan ya shiga kunnuwan su Baba, ba tare da ina kusa ba.” (shafi na 60).

Za mu kammala