Wutar lantarki: Buhari ya sha alwashin bincikar yadda aka kashe Dala biliyan 16

Shugaban Kasa Muhammdu Buhari ya sha alwashin bincikar yadda aka kashe Dala biliyan 16 wajen gyara wutar lantarkin kasar nan a lokacin mulkin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo. Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya je yakin zabe a Jihar Bayelsa. A cewarsa, “Lokacin da muka karbi mulki a shekarar 2015, mun […]

Wutar lantarki: Buhari ya sha alwashin bincikar yadda aka kashe Dala biliyan 16

Shugaban Kasa Muhammdu Buhari ya sha alwashin bincikar yadda aka kashe Dala biliyan 16 wajen gyara wutar lantarkin kasar nan a lokacin mulkin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya je yakin zabe a Jihar Bayelsa.

A cewarsa, “Lokacin da muka karbi mulki a shekarar 2015, mun yi  wa ’yan Najeriya alkawarin samar da tsaro da habaka tattalin arziki da samar da ababen more rayuwa, sannan muka dauki alkawarin tabbatar da cewa dukan masu rike da mukaman gwamnati suna yi wa mutane bayani. Muna fuskantar kalubale a yaki da cin hanci, amma kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba, sannan muna kokarin samar da wutar lantarki.

“Gwamnatocin da suka wuce sun cewa sun kashe wa wutar lantarki Dala biliyan 16, amma tambaya a nan ita ce ina wutar take? Ina aka kashe kudin? Za mu bibiye su, kuma da yardar Allah za kwato kudinmu,” inji shi.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa