Wutar Lantarki: Katse layin KEDCO a Kano somin-tabi ne —TCN
Sassan Kano sun yi kwanaki cikin duhu bayan da TCN ya katse layin wutar KEDCO da suke kai
Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Kasa (TCN) ya ce katse wutar da ya yi wa Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na KEDCO a Jihar Kano somin-tabi ne.
Wasu sassan Jihar Kano sun yi kwanaki a cikin duhu bayan TCN ya katse layin wutar da suke kai saboda taurin bashin da yake bin KEDCO.
TCN ya katse wasu layikan wutar KEDCO mai kula da jihohin Kano da Jigawa da Katsina bayan kokarinsa na ganin kamfanin ya biya bashin ya faskara.
- Yakin Sudan: Najeriya ta tura jirgin soji don kwaso ’yan kasarta
- Sarautar Kano: Dawo da Sanusi II yana hannun Abba —Kwankwaso
Mataimakin Janar-Manajan TCN na Shiyyar Kano, Bello Muhammad da kuma kakakin KEDCO, Sani Bala Sani, sun tabbatar cewa TCN ya katse wutar a ranar 26 ga watan Afrilu da muke ciki.
Layukan wutar da TCN ya katse a Kano su ne Club Road da CBN da kuma Flour Mills (Dan Agundi), wanda hakan ya jefa yankunan da ke samun wuta daga nan a cikin duhu na tsawon kwanaki.
Tun ranar 24 ga wata Babban Jami’in Kasuwanci na TCN, E. A. Eje ya sanar cewa, “TCN ya ba da umarnin katse wutar KEDCO saboda saba ka’idar biyan bashi.”
Ya bayyana cewa katse layikan somin-tabi ne kafin TCN ya katse wutar gaba daya idan kamfanin bai biya bashin ba.
Ya ce, “Mun riga an sanar da KEDCO da duk wadanda ake bi bashi game da saba alkawarin nasu.
“ Mun kuma wallafa a jarida inda muka bayyana ranar da za mu yanke musu wuta bisa tsarin kasuwancin, kuma har wa’adin ya wuce.”
Amma mai magana da yawun KEDCO, Sani Bala Sani, ya ce, “Duk da haka, kamfanin na aiki tare da TCN da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin an daidaita nan ba da jimawa ba.”
Sani ya ba wa jama’a hakuri, da alkawarin tabbatar da sama musu wutar lantarki mai inganci.