Wutar lantarki ta kashe barawon taransufoma

Al’ummar unguwa sun wayi gari da ganin gawar barawon tana lilo a jikin turakun wutar lantarki

Wutar lantarki ta kashe barawon taransufoma

Wasu turakun wutar lantarki

Wutar lantarki ta kashe wani barawon tiransufoma a unguwar Jattu da ke Karamar Hukumar Etsako ta yamma a Jihar Edo.

Al’ummar unguwar dai sun wayi gari ne da ganin gawar barawon da ake zargi, tana lilo a jikin turakun wutar lantarki da ke hada da tiransfomar.

Sai da wanda ake zargin ya yanke wayoyin da ka karkashin tiransufomar, ya ajiye su a gefe, sannan ya hau sama zai yanko dogayen wayoyin da ke raba wutar, inda a nan ne ya gamu da ajalinsa.

Shaidu sun bayyana cewa daga bisani jami’an Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Edo (BEDC) sun zo sun dauke gawar suka tafi da ita.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Chidi Nwabuzor, dai ya ce ba shi da labarin abin da ya faru.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos