Wutar lantarki ta kashe mutum 2 a Jos

An tabbatar da mutuwar mutum biyu sanadiyyar tangardar wutar lantarki a mahadar Dadin Kowa da ke Jos ta Kudu a jihar Filato. Majiyarmu ta gano cewa, wadanda suka rasun matasa ne masu aikin gini da ke ginin sabon bankin United Bank for Africa (UBA), da ake ginawa a unguwar Dadin Kowa lokacin da hadarin ya […]

Wutar lantarki ta kashe mutum 2 a Jos

Turakun wutar lantarki

An tabbatar da mutuwar mutum biyu sanadiyyar tangardar wutar lantarki a mahadar Dadin Kowa da ke Jos ta Kudu a jihar Filato.

Majiyarmu ta gano cewa, wadanda suka rasun matasa ne masu aikin gini da ke ginin sabon bankin United Bank for Africa (UBA), da ake ginawa a unguwar Dadin Kowa lokacin da hadarin ya faru.

Hadarin wutar lantarkin ya rutsa da matasa uku  ne biyu daga ciki suka rasu dayan kuwa jinya a asibiti.

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta

Sojoji sun daƙile yunƙurin mayaƙan ISWAP a Borno