Wutar Lantarki ta Kashe Uwa da Da da Makwabcinsu A Ogun
Wutar lantarki ta hallaka wata mata da danta da wani mutum guda a kasuwar Mowe da ke Karamar Hukumar Obafemi-Owode a Jihar Ogun
Wutar lantarki ta hallaka wata mata da danta da wani mutum guda a kasuwar Mowe da ke Karamar Hukumar Obafemi-Owode a Jihar Ogun.
Gobarar ta tashi ne sakamakon matsalar wutar lantarki bayan da aka dawo da wutar sa’o’i kadan bayan an yi ruwan sama a ranar Lahadi.
Shaidu sun ce, wutar ta tashi ne daga wata tiransfoma a kusa da shagon bayan ’yan kasuwa sun sun fara fara gudanar da harkokinsu na yau da kullum a kasuwar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa baya ga mutum uku da suka mutu, wasu hudu sun jikkata sakamakon gobarar.
Daraktan yada labaran Karamar Hukumar Obafemi Owode, Segun Soneye, ya shaida wa Aminiya cewa matar ta kone kurmus.
Segun Soneye ya dora alhakin faruwar lamarin a kan ginin shaguna da aka yi a karkashin wayar wutar lantarki.
Ya ce shugaban karamar hukumar Lanre Ogunsola ya ziyarci masu shagunan da abin ya shafa inda ya jajanta masu kan lamarin.
Tuni dai shugaban karamar hukumar ya bai wa masu shagunan wa’adin kwanaki bakwai su tashi daga shagunan da aka gina a karkashin babban layin wutar lantarki a gefen tashar wutar lantarki domin kauce wa sake afkuwar hakan.
Shugaban karamar hukumar ya ziyarci wadanda lamarin ya rutsa da su, da ke karbar magani asibitin Mowe, ya kuma ba su tabbacin kula da lafiyarsu daga aljihun gwamnati.
Kakakin ’yan sandan Jihar Ogun, Omolola Odutola, ya tabbatar da faruwar lamarin.