Wutar lantarki ta yi ajalin uwargida da amarya a Neja

Wata uwargida da amaryarta, sun rasa ransu bayan da wutar lantarki ta ja su a kauyen Tungan Wakili da ke karamar Hukumar Tafa ta Jihar Neja a ranar Alhamis din makon jiya.Lamarin ya faru ne bayan daukewar ruwan sama a yankin kamar yadda mijin matan Malam Umaru Sadau ya shaida wa wakilinmu. Ya ce da […]

Wutar lantarki ta yi ajalin uwargida da amarya a Neja
Wutar lantarki ta yi ajalin uwargida da amarya a Neja

Wata uwargida da amaryarta, sun rasa ransu bayan da wutar lantarki ta ja su a kauyen Tungan Wakili da ke karamar Hukumar Tafa ta Jihar Neja a ranar Alhamis din makon jiya.
Lamarin ya faru ne bayan daukewar ruwan sama a yankin kamar yadda mijin matan Malam Umaru Sadau ya shaida wa wakilinmu. Ya ce da farko uwargidarsa Hajara ce ta fara fuskantar matsalar jan a lokacin da take kokarin shanya wani tsumma da ta yi amfani da shi wajen tsantsame ruwan da ya shiga dakinta.
Malam Umaru Sadau wanda shi ne mai unguwar yankin, ya ce sanya tsumman a kan igiyar shanyar ke da wuya sai ta yiwo kasa ta baya sakamakon jan wuta daga igiyar wanda ta hadu da wayar wutar lantarkin gidan ba tare da sun sani ba. Ya ce abokiyar zamanta mai suna Salamatu na ganin haka, sai ta nufi wajen a guje don ta tallafa mata, amma ita ma sai ta fadi ta rasu nan take bayan igiyar wadda ta riga ta tsinke, ta fada a kan wuyarta. Ya ce uwargidar ita ma ta rasu daga baya a bayan rasuwar amaryar.