‘Wutar lantarki za ta wadata a watan gobe’
Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya ce za a ci gaba da fuskantar rashin wadatacciyar wutar lantarki da karancin mai a kasar nan har zuwa watan gobe (Mayu) sakamakon ta’adin da ‘yan ta’adda suka yi wa tashar samar da iskar gas da man fetur da ke garin Forcados a Jihar Delta. Ya sanar da hakan ne […]

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya ce za a ci gaba da fuskantar rashin wadatacciyar wutar lantarki da karancin mai a kasar nan har zuwa watan gobe (Mayu) sakamakon ta’adin da ‘yan ta’adda suka yi wa tashar samar da iskar gas da man fetur da ke garin Forcados a Jihar Delta.
Ya sanar da hakan ne bayan ya ziyarci inda a ka yi ta’addin, kuma ya bukaci gaggauta aikin gyara tashar wadda take samar da kashi 40 cikin 100 na iskar gas din da ake bukata don samar da wutar lantarki a kasar nan.