Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke karo na 4 a 2024

Wannan shi ne karo na huɗu da wutar lantarki ke ɗaukewa a Najeriya a 2024.

Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke karo na 4 a 2024

Wutar lantarki ta dauƙe gaba ɗaya a faɗin Najeriya sakamakon durƙushewar babban layin lantarkin ƙasar.

Wutar lantarkin ta sake ɗaukewa gaba ɗaya ne, bayan da ta ragu zuwa 0.80 a ranar Asabar.

Binciken da aka yi a shafin intanet na kamfanin da ke kula da wutar lantarkin ya nuna yadda ya fara raguwa da misalin ƙarfe 2 na rana zuwa megawat 2,797.16.

Ƙarfin wutar lantarki ya ƙara raguwa zuwa 1,020.08 da misalin ƙarfe 3 na rana kafin ya ƙasa sosai zuwa 0.80 da misalin ƙarfe 4 na yamma.

Aminiya ta ruwaito cewa 0.80 shi adadin abin da babban layin samar da wutar lantarki ke da shi a yanzu haka.

Wannan shi ne karo na huɗu da babbar tashar samar da wutar lantarki ta Najeriya ke faɗuwa a 2024.

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano