Xan jarida ya zama Shugaban kulob xin Warri Wolves

Tsohon xan jarida mai rubuta labarin wasanni a Jihar Delta Moses Etu ya zama sabon shugaban qungiyar qwallon qafa ta Warri Wolves.Bayanin haka na qunshe ne a wata sanarwa da gwamnatin Jihar Delta ta fitar jim kaxan bayan ta rushe hukumar gudanarwar kulob xin da ke qarqashin Davidson Uwumi inda ta maye gurbinsu da sababbi.Mista […]

Xan jarida ya zama Shugaban kulob xin Warri Wolves
Xan jarida ya zama Shugaban kulob xin Warri Wolves

Tsohon xan jarida mai rubuta labarin wasanni a Jihar Delta Moses Etu ya zama sabon shugaban qungiyar qwallon qafa ta Warri Wolves.
Bayanin haka na qunshe ne a wata sanarwa da gwamnatin Jihar Delta ta fitar jim kaxan bayan ta rushe hukumar gudanarwar kulob xin da ke qarqashin Davidson Uwumi inda ta maye gurbinsu da sababbi.
Mista Moses Etu a da shi ne jami’in hulxa da jama’a na qungiyar, a yanzu ya samu wannan xaukaka ce bayan da gwamnati ta nemi da ya yi amfani da basirarsa wajen xaukaka martabar kulob xin musamman a wannan lokaci da kulob xin zai fafata a gasar zakarun kulob-kulob na Nahiyar Afirka (CAF Champions League) wanda za a fara a watan gobe.
Haka kuma gwamnatin ta buqace shi da ya yi duk mai yiwuwa don ganin kulob xin ya lashe wani kofi a karon farko tun bayan da aka qirqiro kulob xin a shekarun baya.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa