Xan shekara 6 ya mallaki Dala miliyan 11 a shekara guda a Amurka

Wani  yaro dan  shekara 6  da  haihuwa  ya  samu  kudi  wuri na gugan wuri  har  Dalar Amurka  miliyan 6  a cikin shekar daya. Abin da  yaron ke yi shi ne  za a kawo  masa kayan wasan yara da suka hada  da  diyan bebi  na roba da  makamantansu yana bayyana  yadda suke da yadda aka yi  […]

Xan shekara 6 ya mallaki Dala miliyan 11 a shekara guda a Amurka

Wani  yaro dan  shekara 6  da  haihuwa  ya  samu  kudi  wuri na gugan wuri  har  Dalar Amurka  miliyan 6  a cikin shekar daya.

Abin da  yaron ke yi shi ne  za a kawo  masa kayan wasan yara da suka hada  da  diyan bebi  na roba da  makamantansu yana bayyana  yadda suke da yadda aka yi  su  da  abin da aka yi su da shi da tasirinsu  ga  yara kamar shi. Duk ’yar tsana ko bebin roba mai kama da mace ko namiji  ko  kuma jirgi ko mota ko wanda  yara ne ke amfani  da shi, idan ka ba wannan yaro mai suna Ryan zai maka bayani game da shi.

Tun yana yi cikin gida iyayensa, har ya fara  janyo  hankalinsu suka  fahimci abin da yake fadi yana da ma’ana  da kuma tasiri.

Daga nan ne sai  suka yi  tunanin cewa su sa wannan bayani a kafar dora bidiyo na zamani na zamani da ake kira youtube.

Ko  kafin a farga yara ’yan uwansa sun  dabaibaye  wannan yaro a youtube suna bude shafinsa suna kallo.

Daga wannan lokacin ne sai aka samar da shafinsa a youtube, sai aka fara biyansa daga abin da yaran da ke kallon wannan bayanin nasa.

Su kuma iyayensa  basu yi kasa a gwiwa ba domin su nci gaba da saya mashi wadannan kayayyakin  wasan yana ci gaba da yin bayani a kansu daya bayan daya.

Yanzu  haka an mayar  da  wannan  bayani nasa a shafin yara, ya koma  mataki-mataki, wato kamar  fitowa-fitowa, kuma  yara a Amurka  yanzu  sun raja’a ga kallon wannan bayani nashi na kayayyakin wasan.

A cikin shekara guda, an samu yaran da yawansu ya kai biliyan 8 da suka kalli wannan bayani na Ryan,

Kamar  yadda Jaridar Mercury ta ce, kuma wannan yaron ya fara  wannan ne  tun yana  dan shekara 3  wato a shekarar 2015, amma abin ya kankanma ne a shekarar 2016.

Shi ma yana yawan kallon wasannin yara a talabijin da youtube, wasu  daga cikin abin da aka ce ya fi  kallo sun hada da Eban TubeHD, da  kuma Hulyan Maya domin suna  yin wasanni  masu  yawa  a bidiyo.

Masu kididdigan kallon wasa a youtube sun bayyana cewa shi ne na 40 a duk fadin Amurka da ake kallo a shafin youtube na yara.

Masu kididdigan sun bayyana cewa ba yara ba, hatta  manya idan suna sauraren wannan yaron sukan ji  kamar wani ke wani gefe a boye yana masa bayani, wannan abu yasa yara kusan inda duk suke, idan sun nemi su kalli wani wasan yara, idan nasa bai zo na farko ba, zai zo na biyu.

Iyayen suka ce tun suna lissafin kayayyakin wasannin da ya yi bayani, har yanzu sun bace lissafi, amma  yanzu sun fara tarawa domin gaba.

Wata mata mai suna Lindsay Weiss ta ce duk ranar da ta hana yaron ta kallon Ryan to ranar babu zaman lafiya gidan.

Ta ce yanzu baida wani abin kallo da ya wuce shafin Ryan, sannan ta ce wani lokacin har yakan rika magana da shi a Talabijin, kai ka ce da wani mutun yake magana a sarari.

Iyaye da dama sun aikewa iyayen wannan sako cewa sun gode da aka samar da shafin wannan yaron domin yaransu yanzu sun raja’a wajen kallon wasansa maimakon wani abu da ke da nasaba da rashin da’a,  ko kuma wata mummunar dabi’a.

Ita ko wata  uwa cewa ta yi bayanan kayan wasan  Ryan sun taimaka wa yaronta koyon magana, domin cikin mutane kullun so yake ya ga ya yi wa  jama’a magana yana kwaikwayon Ryan da yadda yake  bayanin kayayyakin wasa.

Ita kuma wata uwa daga  kasar Indiya ce wa ta yi yaron ta ya ce mata yaushe za ta kaishi ya ga Ryan amma sai ta ce masa ai kasarsu daban.

Daga watan Yunin bara zuwa watan Yuni na shekarar 2017 wannan yaron ya samu kudi har Dala miliyan 6 bayan an cire kudin haraji.