Yaƙin Basasa: Gwagwarmayar da na sha don Nijeriya ta kasance ƙasa ɗaya — Gowon
A wannan tattaunawar, tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja a Nijeriya, Janar Yakubu Gowon (murabus) ya bayyana irin ƙalubalen da ya fuskanta a lokacin mulkinsa da ma irin abubuwan da suka faru kafin, a lokacin da kuma bayan yaƙin basasa, yana mai jaddada yaƙininsa na ɗorewar Nijeriya a matsayin ƙasa guda dunƙulalliya. Ka tsaya kai […]
A wannan tattaunawar, tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja a Nijeriya, Janar Yakubu Gowon (murabus) ya bayyana irin ƙalubalen da ya fuskanta a lokacin mulkinsa da ma irin abubuwan da suka faru kafin, a lokacin da kuma bayan yaƙin basasa, yana mai jaddada yaƙininsa na ɗorewar Nijeriya a matsayin ƙasa guda dunƙulalliya.
Ka tsaya kai da fata wajen tabbatar da haɗin kan Nijeriya; me ka yi a lokacin da yaƙin basasa ya ɓarke?
Na taso ne a wani ƙauyen Hausawa da ake kira Wusasa, kuma duk mun san juna a ƙauyen. A wannan ƙauyen tare Kiristoci suke zuwa coci, haka su ma Musulmi tare suke zuwa masallaci, Hausawansu da Yarbawa da sauran ƙailiu. Saboda haka haɗin kan ƙasar nan yana da muhimmaci a gareni.
Na shafa faɗa cewa idan da babu shirin ficewa daga Nijeriya, to da babu abin da zai kawo neman ɓallewa ballantana har a kai ga yaƙin basasa, domin a lokacin an kai matakin da abin a fili yake cewa yankin Kudu maso Gabas na neman ɓallewa daga Nijeriya.
Nauyin da ke kai na a wancan lokacin na buƙatar in tabbatar da cewa ƙasar ta ɗore a matsayin guda kuma dunƙulalliya. Kuma abin da ya faru ke nan.
Nasan irin abin da ya faru a rikice-rikicen wasu ƙasashen Afirka, musamman Kongo, inda na yi aiki har sau biyu kuma na ga irin zubar da jini da wahalar da al’umma suka sha. Ban sani ba ashe bayan ’yan shekaru ni ma zan fuskaci irin wananna matsala. Don haka dole muka yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da ƙasar nan a matsayin guda ɗaya.
Ina tabbatar muku cewa ba da son rai aka yi ba, sai domin a tabbatar da ganin cewa za mu iya ci gaba da zama tare da juna bayan an magance matsalar; wannan shi ne abin muka yi ke.
An ba wa sojoji jerin wasu umarni da hani, irin su dokokin Yarjejeniyar Geneɓa da sauran dokokin ƙasa da ƙasa da shuka danganci rikice-rikice. Akwai dokoki 12 da suka haɗa da rashin yaƙar tsofaffi da mata da ƙananan yara da sauransu. Waɗanda suka ɗauki makami kaɗai za a yaƙa. Amma abin takaici sai aka samu akasin hakan.
Da za ka samun wata dama, wane mataki za ka ɗauka na daban?
Ba na tunanin akwai wani abu na daban da zan yi, saboda an yi duk ƙoƙarin da ya dace domin ganin ƙasar ba ta rabe ba. Mas’uliyya ce a kaina in tabbatar hakan bai faru ba. Haka muka shekara biyu muna yaƙi tare da tabbatar da ganin ba a yi mana katsalandan daga ƙasasahen waje ba.
A namu rikicin babu maganar barin dakaru ko gwamnatin wata ƙasa ta tsoma baki, saɓanin rikicin Kongo inda aka tura rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ciki har da sojojin Nijeriya da na wasu ƙasashen Afirka domin shawo kan rikicin.
Haka muka shawo kan tamu matsalar muka kuma tabbatar da cewa mun ci gaba da rayuwa tare da juna a matsayin al’umma guda. Don haka ba na tunanin akwai wani abu daban da zan yi, wanda ba wannan ba.
Har yanzu a yankin Kuda maso Gabas ba a daina fafutukar neman kafa ƙasar Biafra ba. Shin yarjeniyoyin (3Rs) da aka cimma bayan yaƙin basasa ba su yi wani tasiri ba ke nan? Mene ne kuma saƙonka ga al’ummar yankin?
3 Rs na nufin an yi sulhu, kuma ba na tunanin wani abu saɓanin hakan da zan yi a wannan lokacin. An yi ƙoƙari domin tabbatar da cewar al’amarin bai yi munin da zai kai ga rabuwar ƙasar ba. Nauyi ne a kaina in tabbatar da cewa wani yanki bai ɓalle ba daga Nijeriya.
Ina nufin 3Rs wato gyara da dawowa cikin al’umma da kuma sake gina rayuwa da ƙasa (3Rs’).
Haƙiƙa umanrina ga sojojin da suka yi yaƙin shi ne, ‘mutanen da kuka yaƙa ’yan uwanku ne maza da mata, don haka yanzu sai ku koma ku dawo sojojin zaman lafiya. Ku yi duk abin da za ku iya yi musu na taimako domin su koma garuruwansu; ku ba su duk taimakon da suke nema’.
Duk da abin da ya faru, ’yan ƙalibar Ibo da dama sun dawo sun ci gaba da zama a Arewa a Kaduna da Kano da Jos da sauran wurare kuma sun iske dukiyoyinsu da suka tsere suka bari, yadda suka bar su, abokansu ’yan Areawa sun adana musu.
Kusan nan take aka damƙa musu kadarorin nasu. Sojoji sun taimaka musu wajen jigilar su domin komawa sassan Nijeriya daban-daban. Uwa uba, babu maganar gurfanar da wani a kotu, an ba wa kowa damar komawa duk inda yake so ya ci gaba da zama ya yi rayuwarsa.
Sannan na ba wa sojoji umarni na musamman, musamman ma hafsoshi daga cikinsu, saboda sun san cewa bai kamata su yaƙi gwamnati ba. Wanann shi ne dalilin da wasunsu suka yi ritaya daga aiki.
A lokacin jami’in gudanarwana shi ne Mista Ukpabi Asika, wani ɗan kishin ɗasa mai hikima kuma na bai shi duk gudummawar da ya nema. Ala misali mun bayar da tallafi domin ganin an buɗe makarantu, akwai kuma na ɓangaren kiwon lafiya da sauransu. Mun yi abubuwa da dama don ganin an fara sasantawa da haɗe kan al’ummar ƙasa ta yadda za su iya komawa duk inda suke so a cikin ƙasar.
Daga cikin saƙonnina ga al’ummar Kudu maso Gabas, shi ne, yaƙin basasa ya ƙare kuma babu Jamhuriyar Biafra, saboda jama’a sun amince su haɗe a matsayin ’yan Nijeriya. Ko so kuke in ce su ci gaba? A’a. Kar ku yi min wanaan tambayar.
Na gode wa Allah a lokacin da yaƙin ya ƙare ba a kama Cif Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu ba, domin kuwa da abin ya yi mini sarƙaƙiya, musamman saboda mutanen da za su so su ga an ɗauki mataki a kansa. Dalili shi ne, saboda na san zan yi abin da zan yi domin tseratar da rayuwarsa.
Na tuna an riƙa kamanta ni da tsohon shugaban Amurka, Abrahama Lincoln. Na kuma tuna lokacin da wani bature mai suna Mista Bartin Dent, wanda ya ba ni wani littafi a kan yaƙin basasar Amurka. Amma saboda abin da ke faruwa a lokacin ban samu karanta littafin ba, sai kusan ƙarshen yaƙin.
Bayan da na karanta littafin sai na ce wa kaina, abin da ke faruwa a Nijeriya yana kama sosai da yaƙin basasar Amurka. Abin na da matuƙar ban mamaki.
Tsakani da Allah, da na samu karanta littafin kafin fara yaƙin basasar Nijeriya, idan wani ya ce so nake in zama kamar Abraham Lincoln, to da wuya in iya cewa babu abin kwatanta ni da shi. Bambancin kawai shi ne a ƙarshe na iya ci gaba da sasanci da kuma ɗorewar ƙasar.
Don haka na ce ban damu ba, ko za a kira ni Abraham Lincoln na Nijeriya, saboda yanayin da muka tsinci kanmu iri ɗaya ne, haka ma irin sakamakon da muka samu.
Akwai wani ɗan jarida farar fata da ya tambaye ni dalilin da nake tunanin yaƙin ya wuce — ba na tunani mutane za su ci gaba da yaƙin sunƙuru? Amma na gode Allah ba a samu hakan ba.
Bari in karkace ɗan kaɗan. Na gode wa Allah da lokacin da yaƙin ya ƙare, ban kama Cif Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu ba, domin da abin zai yi min wuya. Domin kuwa akwai jama’a da za su ƙarfafa a hukunta shi. Ni kuma na san cewa da na yi duk abin da zan ceci ransa. Amma kuma, da shi ne ya kama ni fa?
Mun ji labarai iri-iri kan abin da ya faru tsakaninka da Ojukwu a Aburi da ke ƙasar Ghana. Za mu so jin ainihin abin da ya faru daga bakinka. Shin kun yarda a da tsarin tarayya?
To, Ojukwu yakan ce, “A kan Aburi muke tsaye,” ni kuma na ce, “Daga Aburi za ku faɗi.”
Labarin Aburi shi ne, mun yi ƙoƙarin duk abin da za mu iya don mu haɗu a Nijeriya mu warware duk abubuwan baƙin cikin da suka faru na kashe-kashe da rikicin da ya biyo bayan juyin mulkin 15 ga Janairu.
Na shirya zuwa Ibadan a washegari, amma aka sanar da ni cewa ba zan iya tafiya ba saboda akwai liyafa da kwamanda ya shirya wa hafsoshi irina da aka turo, da kuma waɗanda aka sauya wa wurin aiki daga rundunar zuwa wasu wurare.
Don haka, dole in halarci liyafar a daren Juma’a don in tabbata na yi abin da ya dace a wannan runduna. Da dare ta yi muka je tafi liyafar, kuma bayan an ƙare na tafi Ikeja domin in kwana.
Can da tsakar dare sai aka fara hayaniya. Ina tunanin me ke faruwa, amma babu wanda ya gaya min komai. Gashi kuma na shirya karɓar ragamar rundunar da safe. Sai aka fara karakaina da sojoji da motoci a cikin rundunar. Bayan ɗan wani lokaci abin ya lafa. Amma bayan wasu sa’o’i biyu zuwa uku, sai abin ya ci gaba fiye da na farkon.
Aka fara busa bigilar kiran sojoji zuwa babban taro. Ina kallo ta taga don in ga abin da ke faruwa. A lokacin ne na ga ɗaya daga cikin hafsoshi, Kyaftin Martin Adamu, wanda daga baya ya zama Janar, amma yanzu ya rasu. Na gan shi yana wucewa kusa da masaukin wucin gadin da aka ba ni in zauna tun da gidan kwamandan ba a kammala shirya shi ba.
Na tambaye me ke faruwa amma bai ce komai ba, don haka na yanke shawarar in je in gani da kaina. Da muka haɗu da shi na tambaye shi me ya kawo hayaniyar, sai ya ce Janar Aguiyi Ironsi, wanda yake Babban Kwamandan Runduna ne ya zo ya gaya musu cewa akwai wata matsala a cikin gari da ta shafi Firayi Minista Tafawa Balewa da Ministan Kuɗi, Okotie Eboh. Ya ce Janar Ironsi kuma ya zo neman taimako don ganin ko zai iya shawo kan matsalar.
Abin da na fara tunani shi ne, Me ya sa Ironsi zai ba da umarnin? Me ya sa ba kwamandan rundunar ba ne ya ba da umarnin, domin duk wani umarni ya kamata ya biyo ta wurinsa? Kamata ya yi Ironsi ya gaya wa kwamandan runduna, shi zai kuma ya sanar da kwamandan bataliya.
Sai na tambaye shi inda Ironsin yake, ya ce yana filin fareti. Don haka na canza kaya zuwa na farar hula don in ga me ke faruwa. Da muka isa, sai ya ce da ni, so yake wata runduna su shirya su je su magance matsalar. Bayan ya gama, ya ce ko da wata tambaya.
A lokacin ban sani ba, ashe duk manyan hafsoshi abokan karatuna an kashe su ba, irin su Maimalari, Kur Mohammed, Laftanar Kanar Abogo Largema da Yakubu Pam . Ɗaya daga cikin abokaina na kusa, Arthur Unegbe, daga Ozobulu, shi ma an kashe shi.
Daga: Andrew Agbese da Isiaka Wakili Fassarar: Sagir Kano Saleh da Ahmed Ali, Kafanchan
Cikakken rahoton a nemi Jaridar AMINIYA.