Ya ƙone budurwa saboda ta ƙi auren shi

Ya yanke hukuncin bayan da bazawarar tasa ta ƙi amincewa da aurensa.

Ya ƙone budurwa saboda ta ƙi auren shi

Zama Kotu. (Hoto: Aminiya)

An gurfanar da wani mutum mai suna Abdullahi Idris, a gaban kotun shari’ar Musulunci a Jihar Kano, saboda zargin ƙone budurwarsa, Sa’adatu Ibrahim, saboda ta ƙi amincewa da aurensa.

Idris, wanda yake zaune a garin Rimi, ƙaramar hukumar Sumaila, ya kasance yana soyayya da Sa’adatu, wadda bazawara ce.

Ya shafe tsawon kwanaki bakwai yana muradin ta amince da batun aurensa amma ta ƙi amincewa da buƙatar tayin da ya mata.

An tuhume shi da laifin yin sharri, ƙone mutum, da yunƙurin kisan kai, sai dai duk da haka ya musanta dukkanin tuhume-tuhumen da ake masa.

Lauyan mai shigar da ƙara, Barrista Maryam Jubril, ta nemi a ɗage shari’ar zuwa wani lokaci.

Sibil Difens ta kama mutum 10 kan aikata laifuka daban-daban a Gombe

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe

Mata sun yi zanga-zanga gabanin rantsar da Trump a Amurka

TikTok ya daina aiki a Amurka