Ya ba karnuka 300 muhalli don kare su daga guguwa

Hakan ya sa masoya dabbobi suka kira shi da ‘Jarumi’ bayan ya wallafa wannan labari.

Ya ba karnuka 300 muhalli don kare su daga guguwa

Ricardo da karnukan a gidansa

Wani mai kare hakkin dabbobi a kasar Mexico mai suna Ricardo Pimentel, ya samar wa sama da karnuka 300 muhalli a gidansa don kare su daga guguwa.

A ranar 7 ga Oktoba da misalin karfe 5:30 na asuba ne guguwar ta rusa gine-gine a Jihar Kuintana Roo da ke Mexico, sai dai awanni kafin guguwar, Ricardo Pimentel wanda ke zaune a birnin Leona Bicario kuma yake kare ’yancin dabbobi, ya yi ta kokarin samar da muhalli ga dabbobin a gidan Tierra de Animales don kare su daga guguwa da ruwa mai karfi a yankunan da suke.

Wannan ya sa masoya dabbobi suka kira shi da ‘Jarumi’ bayan ya wallafa wannan labari.

Babban abin da Ricardo ya yi shi ne ya cika gidansa da karnuka sama da 300, tare da kuregu da wasu dabbobi da suka hada da jinsin mage da kaji da zomaye da wasu dabbobin don kare su daga da guguwar.

“Idan zan iya samar wa sama da karnuna 300 da kyanwoyi da kuregu da zomaye muhalli, wa ya san adadin dabbobin da suke gidana?

Saboda kada su kasance a wani yanayi na rashin muhalli don haka na tanadar wa karnuka da sauran dabbobin da ba su da gida muhalli har sai annobar ta wuce,” Ricardo ya wallafa a shafinsa na Facebook.

An wallafa hoton Ricardo Pimentel lokacin da karnukan suka yi masa zobe, inda hotunan suka janyo muhawara a shafin sada zumunta na zamani na Latino kuma hakan ya sa masu yin sharhi suke ta jinjina gare shi tare da bayyana shi a matsayin jarumi.

Fitattun mutanen da ake bibiya a kafofin yada labarai a duk duniya suna ta watsa hotunan jarumin kan sadaukar da rayuwarsa wajen ceton rayuwar dabbobin.

Bayan aukuwar guguwar Ricardo ya bukaci masoya dabbobin su bada tallafinsu wajen ciyar da dabbobin kamar samar da abincin karnuka da na kyanwoyi da kayan tsabtace muhallin da ake kula da dabbobin da kayan marmari da tsabar kudi da sauran abubuwan da za a iya bukata don inganta rayuwar dabbobin a gidan Tierra de Animales

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7