Ya ba mata 1000 tallafi don murnar nasarar Buhari da Masari
Wani matashi mai suna Alhaji Nura Sani Kadaga da ke zaune a kofar Guga cikin garin Katsina ya ba mata dubu daya (1000) tallafi domin nuna jin dadi da farin cikikan nasarar da Janar Muhammadu Buhari da Aminu Bello Masari na Jam’iyyar APC suka samu a zaben Shugaban kasa da kuma Gwamnan Jihar Katsina. Alhaji […]
Wani matashi mai suna Alhaji Nura Sani Kadaga da ke zaune a kofar Guga cikin garin Katsina ya ba mata dubu daya (1000) tallafi domin nuna jin dadi da farin cikikan nasarar da Janar Muhammadu Buhari da Aminu Bello Masari na Jam’iyyar APC suka samu a zaben Shugaban kasa da kuma Gwamnan Jihar Katsina.
Alhaji Nura wanda ya ce shi ba dan siyasa ba ne kuma ba ya bukatar komai daga wurin wadanda suka ci zaben, ya ce ya yi haka ne don murna a kan yadda Allah Ya sa aka yi zaben cikin kwanciyar hankali da lumana da yadda Allah Ya karbi addu’o’in bayinSa ta raba su da halin da suke ciki karkashin mulkin Shugaba Jonathon da jam’iyyarsu ta PDP, lamari da ya ce ba karamin abin farin ciki ba ne tare da yi wa Allah godiya.
Alhaji Nura ya ce, “Maimakon in yanka wata dabba don nuna farin cikina sai na ga ya dace in samu wasu bayin Allah da zan taimaka mawa duk kuwa da kankantar abin da za su yi amfani da shi fiye da kwana daya. Na kuma yanke shawarar taimaka wa mata ne saboda su ne suka fi neman taimako saboda su ke tare da yara, kuma wasu daga cikin matan ba su da maza ko suna tare da marayu.”
Kayan da Alhaji Nura ya raba sun hada da sabulan wanka da na wanki, wasu kuma har da tufafi.
Dukkan macen da ta samu wannan tallafi sai Alhaji Nura ya hada mata da Naira dari biyar (N500).
Matashin ya yi kira ga masu hannu da shuni kuma masu son nuna farin cikinsu a duk lokacin da wani abin murna ya samu, su rika samun wani abin da za su rika tallafa wa mabukata, maimakon yin hidimar da za ta tsaya a cikin gidajensu. “Za a kashe makudan kudi wajen yin abincin da bai wuce mutane kalilan ne kadai za su ci ba, wanda inda za a yi amfani da wannan kudin wajen taimakawa, mabukata da yawa za su amfana, inji Nura Kadaga.