Ya babbaka matarsa saboda zuwa gidan biki

A karshen makon jiya ne jama’ar unguwar Olomore a Abeokuta suka wayi gari da labari mai tada hankali na wani magidanci mai suna Keji Osunjinrin da ya hallaka uwargidansa Fatimi Osinjinri  har lahira ta hanyar babbaketa da wuta , abin da ya tayar da hankulan daukacin mazauna yankin.Mijin ‘yar uwar  Fatimo, wanda ya ki ya […]

Ya babbaka matarsa saboda zuwa gidan biki

g Keji Osunjinrin, wanda ake zargi da babbaka matarsaA karshen makon jiya ne jama’ar unguwar Olomore a Abeokuta suka wayi gari da labari mai tada hankali na wani magidanci mai suna Keji Osunjinrin da ya hallaka uwargidansa Fatimi Osinjinri  har lahira ta hanyar babbaketa da wuta , abin da ya tayar da hankulan daukacin mazauna yankin.
Mijin ‘yar uwar  Fatimo, wanda ya ki ya ambaci sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa ta halarci bikin suna ne na haihuwar da kanwarta ta yi, wacce mata ce a gare shi,  “ takaddama ta kaure a tsakanin ma’auratan a lokocin da  ta halarci bikin radin suna da ya gudana a gidana da safiyar lahadi , sai mijin nata ya kira ta ta waya ya ce mata ta yi maza ta koma gida domin yana nan tafe, sai ta ce masa ai tana so ta je wani bikin baya ga na gidana ,  nan take ya bayyana mata  rashin yardarsa, ya kuma sha alwashin daukar  mataki a kanta mudin ba ta koma gida a kan kari ba ,  bayan da ya samu labarin halartarta  wurin bikin sai ya koma gida a makare  dauke da man fetur a jarka, inda ya iske ta a dakin dafa abinci tana  girki, nan fa ya kwara mata fetur ya kuma banka mata wuta,  kafin daga bisani ya garzaya da ita asibitin  Aki Olubgade, inda ta cika bayan kwana daya da faruwar lamarin” inji shi.
Wanda ake zargi Keji Osunjinrin, wanda fitaccen dan siyasa ne a yankin Olomore da Itaushi a Abeokuta, ya bayyana cewa, ba da gangan ya kone matarsa ba, hasalima dai ya sayo man fetur ne yana kokarin zubawa a injin janareto sai ya fantsama a jikinta  ta kama da wuta a lokacin da take girki a dakin dafa abinci, lamarin da ‘yan uwan matarsa  suka musunta, domin a cewarsu, ta yaya za a ce gobara ce ta tashi kuma shi wanda yake dauke da fetur din ba ta kona shi ba, haka zalika jarkar man fetur  din ma ba ta kone ba, shi kuma ya  tsira babu ko kwarzane a jikinsa.
Makwabtan gidan da lamarin ya faru, wadanda suka nemi a sakaye sunayensu, sun shida wa Aminiya cewa a lokacin da Keji ya banka wa Fatimo wuta akwai makwabciyarta da ita ma take girki a kusa da wajen, wacce ita ce ta shaida lamarin da ya faru. Sai dai duk kokarin da Aminiya ta yi domin jin ta bakinta lamarin ya ci tura, domin ta yi gum da bakinta ba ta ce uffan ba, haka zalika da yawa daga cikin makwabtan sun ki su yi magana da ‘yan jarida.
A lokcin da  wakilinmu ya ziyarci asibitin da marigayiyar ta cika ya tarar da mijin nata, wanda shi ne ya garzaya da ita asibitin, tare da ‘yan uwanta wadanda suka nemi jami’an asibitin su ba su gawarta  a kuma rufe maganar ta kare a nan , ana cikin haka ne sai wani shashe na ‘yan uwan nata suka ga bai dace su bari abin ya wuce haka ba,  suka kuma tsaigunta wa jami’an ‘yan sanda wadanda suka iso suka kame mai laifin suka kuma yi gaba da gawar .
.Jami’in hulda da jama’a na rundunar  ‘yan sandan yankin da lamarin ya abku, Abimbola Oyeyemi ,ya tabbatar da faruwar lamarin, kana ya kara da cewa an kai ajjiyar gawar matar a wani gidan adana gawa da ya ki ya bayyana shi, domin gudanar da bincike, kuma tuni rundunar ‘yan sandan ta kame wanda ake zargin, inda za a  cigaba da bincikensa a hedikwatar ‘yan sandan jihar  Ogun da ke Eleweron, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu da zarar an kammala bincike.