Ya banka wa kansa wuta a kan rashin abun Kirsimeti

Wani magidanci mai suna Fredrick Onigbo da matsalolin rayuwa suka dabaibaye shi ya kashe kansa ta hanyar banka wa kansa wuta kwana biyu kafin ranar kirsimeti. Fredrick Onigbo, mai  shekara 50, wanda dan asalin karamar Hukumar Ogwu ne da ke jihar Enugu, an hango shi yana cin wuta ne da misalin karfe 7 na ranar litinin […]

Ya banka wa kansa wuta a kan rashin abun Kirsimeti

MARIGAYI Mista Fredrick tare da matarsa a lokacin da yake rayeWani magidanci mai suna Fredrick Onigbo da matsalolin rayuwa suka dabaibaye shi ya kashe kansa ta hanyar banka wa kansa wuta kwana biyu kafin ranar kirsimeti.
 Fredrick Onigbo, mai  shekara 50, wanda dan asalin karamar Hukumar Ogwu ne da ke jihar Enugu, an hango shi yana cin wuta ne da misalin karfe 7 na ranar litinin din makon jiya, a wani waje da ke cike da haki a gefen Unguwar Gwarinpa. Kafin a shawo a kashe wutar ta riga ta jikkata shi har ya rasa ransa.
Wani da ya kasance cikin wadanda suka yi yunkurin ceto ran mamacin mai suna Ezra Daniel, da ke sana’a a kusa da gidan man NNPC na Gwarinpa, ya bayyana wa wakilinmu cewa, “ ina tare da wadansu a inda nake sana’a sai muka hango wuta tana ci a bayan gidan man NNPC, muka garzaya wajen cikin hanzari don shawo kan wutar, a lokaci ne wani daga cikinmu sai ya ce ga fa mutum yana cin wuta, yana tsalle-tsalle, nan da nan muka maida hankali a kansa tare da kashe wutar, sai dai kashe wutar ke da wuya sai ya cika, sannan aka sanar da ’yan sanda, wadanda suka wuce da gawarsa zuwa wani waje.
Wakilinmu ya zanta da matar marigayin mai suna Misis Uchechukwu Onigbo a gidansu na haya da ke yankin Gwarinpa billage a Gwarinpa Abuja. Misis Uchechukwu wadda ke tare da ’yar uwar marigayin da ta zo daga Kaduna tare da uku daga cikin ’ya’yayensu bakwai. A yayin zantawar, ta bayyana cewa, mijin nata wanda ke sana’ar tukin tasi, ya jima ba shi da aikin yi saboda lalacewar motarsa, wadda ya saye ta tsohuwa bayan dakatar da sana’ar achaba a wannan yanki na Abuja.
Ta ce, ya ranto bashi ne daga banki da nufin gyara motar amma burinsa bai cika ba, saboda cinye kudin da ta ce kanikawa suka yi ba tare da biyan bukata ba, “jami’an banki sun yi ta matsa masa a kan rashin fara biyan kudin, ga matsalar kudin haya na gida, wanda shekara guda ke nan yanzu masu gidan wadanda gwarawa ne ke binmu, ga matsalar kudin makaranta na yara 6, wanda saboda rashin biya aka hana su rubuta jarrabawar baya, a sakamakon haka sun daina zuwa makaranta, ga matsalar yadda zai binne mahaifiyarsa da ta rasu tun a watan Nuwambar da ta gabata a jiharmu ta Enugu, wadannan matsaloli sun dade suna damunsa.’’
EZRA Daniel ke nuna inda suka hango gawar na cin wutaMatar marigayin wanda ke da rumfa a kasuwar Gwarinpa billage inda ta ke sayarda kayan abinci, ta ce marigayin na taya ta zama a wadansu lokuta, idan ya rasa abin da zai yi. Ta ce a ranar da Mista Fedrick ya rasa ransa, ta farka da safe ba ta ganshi ba bayan sun kwana a daki guda, “Da farko na dauka ya je garejin unguwar nan ne inda yake neman aikin rikon tuki ko leburanci, kamar yadda ya saba, amma da na ga abun ya dauki lokaci ba tare da ganin dawowarsa ba, sai na buga wa ’yar uwarsa da ke Kaduna waya a kan al’amarin inda ta garzayo nan kashegari. Daga nan ne kuma muka sanar da al’amarin ga babban ofishin ’yan sanda na Gwarinpa, inda na cika wata takarda.’’
 Ta ci gaba da cewa, “sai dai daga baya na fahimci ’yan sanda na da labarin gano gawar, amma sai suka ki sanar da ni, sai bayan bikin kirsimeti da kwana 2 sannan suka kira ni ta waya suka sanar da ni, inda suka ce sun jinkirta shaida min al’amarin ne don ba ni damar yin kirsimeti ba tare da bakin cikin rashin miji ba. Sai dai ban samu kwanciyar hankali ba, saboda mijina bai taba bari na haka ba, haka dai na yi ta zama a cikin zullumi.’’
Matar  marigayin, wadda mamba ce a majami’ar Christ Redemption Praying Ministries Gwarinpa, a yayin da mijin nata kuma yake halartar Holy Cross Catholic Church, ta ce kafin mutuwar tasa, ya jima yana koka mata a kan matsalar rayuwa, inda take ba shi hakuri. Ta ce, sun kwashe shekara 13 a Abuja tare da mijn nata da suka yi aure tun a jiharsu ta Enugu, kuma babban abin da ke damunta a yanzu shi ne yadda za a dauki gawar marigayin daga asibitin Kubwa inda aka kai ajiyarta zuwa jihar tasu, sai kuma yadda za ta rike ’ya’yansu bakwai da ya barta da su, inda ta bukaci jama’a da su kawo musu dauki.  
MATAR marigayin tare da uku daga cikin ‘ya’yansu bakwai a yayin zantawarta da AminiyaBabbar jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ’yan sanda ta Abuja, DSP Hyelhira Altine Daniel wadda ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce rundunarsu ta amshi binciken al’amarin daga babban ofishinsu na Gwarinpa don ci gaba da bincike.