Ya banka wa kansa wuta saboda budurwa
Wani matashi mai suna Mustapha Adamu, mazaunin unguwar dandago a yankin karamar Hukumar Gwale cikin Jihar Kano ya banka wa kansa wuta saboda kasa shi da aka yi wajen neman auren budurwarsa wacce suka shafe tsawon lokaci suna soyayya.Lamarin mai kama da almara ya faru ne a ranar Asabar da daddare, inda matashi Mustapah Adamu, […]

Wani matashi mai suna Mustapha Adamu, mazaunin unguwar dandago a yankin karamar Hukumar Gwale cikin Jihar Kano ya banka wa kansa wuta saboda kasa shi da aka yi wajen neman auren budurwarsa wacce suka shafe tsawon lokaci suna soyayya.
Lamarin mai kama da almara ya faru ne a ranar Asabar da daddare, inda matashi Mustapah Adamu, wanda shekarunsa ba su wuce 27 ba, ya je gidan budurwar tasa mai suna Hindatu Alhassan a unguwar dandago, ya aika a kira ta amma bai samu damar ganinta ba, hakan ya sa ya aika aka kira masa mahaifiyarta, inda bayan ta fito a gabanta ya duddula wa kansa fetur ya kuma kunna ashana a take wuta ta tashi ta babbake masa dukkanin jikinsa, lamarin da ya sa aka yi gaggawar garzayawa da shi Asibitin kwararu na Murtala Mohammed don ceto ransa.
Wani ganau wanda yana cikin wadanda suka taimak aka kashe wutar da ke tashi a jikin Mustapaha , wanda kuma ya nemi a boye sunansa, ya bayyana cewa, da farko da suka ga matashin da wuta a jikinsa sun yi tsamamnin masu wasan tashe ne, sai daga bisani suka gane abin da yake faruwa, inda suka kai masa dauki. “Muna zaune sai muka ga ya nufo mu wuta na cin jiinsa, da farko mun dauka masu wasan tashe ne, sai daga bisani muka ga ashe Mustapha ne, kasancewar duk mun san shi. A nan ne ‘yan gidan su budurwar tasa suka yi mana bayanin cewa shi ya banka wa kansa wuta . A nan dai muka taru muka kashe masa wutar, inda aka yi gaggawar sanar da ‘yan uwansa tare da daukarsa zuwa Asibitin Murtala.”
Binciken da Aminiya ta gudanar a unguwar dandago ya nuna cewa akwai soyayya mai karfi kuma dadaddiya a tsakanin masoyan biyu, kafiin al’amura su juye, inda ya fuskanci yarinyar da iyayenta sun juya masa baya sakamakon wani saurayi da ya fito yana neman auren budurwa Hindatu, wanda kuma dan uwa ne a gare ta.
Majiyar Aminiya ta rawaito cewa, iyayen budurwa Hindatu sun dade suna bai wa Mustafa dama don ya fito a yi musu aure da ‘yar tasu, lamarin da ya kasa yiwuwa daga bangaren matashi Mustapha. “Ganin iyayen Hindatun sun ba shi dama har kusan karo uku amma ya kasa fitowa a yi auren, hakan ya sa su kuma suka ba wani dan uwanta damar neman aurenta, lamarin da bai yi wa Mustapha dadi ba, har a karshe ya dauki wannan mummunan mataki a kansa.” Inji majiyarmu.
Wata majiyar tamu ta kusa da matashin ta rawaito cewa abin da ya hana matashi Mustapha fitowa a yi aurensa da Hindatu shi ne kasancewar iyayensa sun nuna rashin amincewarsu a kan auren. “Gaskiya ne iyayensa ne suka jawo masa wannan lamarin, saboda ya dade yana son auren yarinyar amma suka ki yarda da auren. Mu dai a unguwa mun samu labarin cewa wai dabi’arta ce ba su gamsu da ita ba.’’
Malama Hafasatu Alhassan it a ce mahaifiyar budurwa Hindatu, ta shaida wa Aminiya cewa bayan ta fito soro don amsa kiran Mustapha, suna gaisawa za su yi magana sai kawai ta ga wuta ta tashi a jikinsa. “Da yake da daddare ne ga duhu a soronmu ban san abin da yake aikatawa ba, ni dai kawai sai ganin wuta na yi ta tashi fal a jikinsa, nan da nan kuma sai wani mashin da ke a soron gidan namu shi ma ya kama da wuta. Hakan ya sa na yi cikin gida a guje ina kiran mutanen gidan tare da sanar musu abin da ya faru. Kafin mu fito har ya fita waje, hakan ya sa muka fito muna jimamin abin da ya aikata. “
Game da batun zargin da ake yi cewa an kasa matashi Mustapaha kuwa, Malam Hafsatu ta bayyana cewa, “gaskiya ne akwai wanda yake nemanta wanda kuma duk da cewar dan uwanta ne ba a kai ga yin maganar auren ba kamar yadda shi Mustaphan yake tsammani. Kuma tun farko ma gaggawa ya yi, saboda kowa ya san ita matar mutum ai kabarinsa ce, kuma shi aure rabo ne. Idan Allah Ya kadarta matarsa ce Hindatu babu makawa sai ya aure ta, haka kuma idan Allah bai kadarta ba duk son ka da abu ba za ka same shi ba. Allah dai Ya zaba abin da ya fi alheri.”
Wani na kusa da matashin mai suna Muhammad Ahmad ya shaida wa Aminiya cewa a ranar da lamarin zai faru matashin ya yi masa korafi game da halin da iyayyen yarinyar suke nuna masa, da kuma labarin da ya samu na neman da wani saurayin yake yi mata. “A ranar da lamarin zai faru da yamma kafin a yi buda-baki sai yake min korafi game da yadda iyayen yarinyar suke masa, inda ko ya je wurita hira ba a bari ya ganta da kuma labarin da ya samu na neman aurenta da wni dan uwanta yake yi. A nan dai muka tattauna batun, cewa idan mahaifiyarsa ta dawo daga Umara za a yi kokarin a kan kudin gaisuwa gidan su yarinyar, don ya samu natsuwa. A nan ne ma yake gaya min cewa idan dare ya yi zai je wurinta. Ni kuma kamar na san hakan za ta faru sai na ce kamata ya yi ya dauke musu kafa na kwana biyu, ya daina zuwa wurinta, idan ma ta yi masa waya ya daina dagawa. To da yake an ce kaddara ta riga fata, sai ga shi ya je har ya aikata wa kansa wannan mummuman aiki.”
Da Aminiya ta yi kokarin tuntubi iyayen matashi Mustapaha a kan batun da ake yadawa cewa su ne suka hana shi auren yarinyar saboda ba sa son yarinyar, ta iske mahaifiyarsa tana kasa mai tsarki don yin umara. Sai dai wata ‘yar uwarsa wacce kuma ta nemai a boye sunanta, ta bayyana cewa sun dauki wannan lamari a matsayin kaddara, don haka babu abin da za su ce a kan lamarin , sai dai su yi masa fatan samun lafiya. “Wanann abu ya riga ya faru, shi ya kona kansa da kansa. Mun dauke shi a matsayin kaddara. Babu abin da za mu ce sai dai mu yi masa fatan samun lafiya tare da addu’ar Allah ya ganar da shi.” Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano ta bakin Kakakinta DSP Magaji Musa Majiya ta tababtar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa a yanzu haka mtashin yana kwance a Asibitin kwararru na Murtala Mohammed yana karbar magani.”A yanzu dai fatanmu shi ne mu ga ya samu cikakkiyar lafiya kafin mu san mataki na gaba da za mu dauka. Wannan dai yunkurin kisan kai ne, wanda kowa ya san hakan babban laifi ne.”