Ya bari kura ta cinye mazakutarsa don ya zama attajiri

Wani dan kasar Malawi da ke zaune a kasar Zambiya yana jinya a asibiti sakamakon sadaukar da mazakutarsa da ’yan yatsun kafarsa ga kura bayan da wani boka ya fada masa cewa muddin yana so ya zama attajiri, sai ya yi haka.Mutumin mai suna Chamangeni Zulu, dan kimanin shekaru 40, yana kwance a babban asibitin […]

Ya bari kura ta cinye mazakutarsa don ya zama attajiri

Wani dan kasar Malawi da ke zaune a kasar Zambiya yana jinya a asibiti sakamakon sadaukar da mazakutarsa da ’yan yatsun kafarsa ga kura bayan da wani boka ya fada masa cewa muddin yana so ya zama attajiri, sai ya yi haka.
Mutumin mai suna Chamangeni Zulu, dan kimanin shekaru 40, yana kwance a babban asibitin kasar Zambiya kusa da iyakar kasar Malawi bayan da ya bar kura ta cinye mazakutar tasa da gangan.
Mista Zulu ya shaida wa mujallar ‘Times’ ta kasar Zambia  cewa bokansa ne ya yi masa alkawarin cewa idan ya sadaukar da wani bangare na gabar jikinsa zai zama hamshakin attajiri.
Ya ce, “Na hadu da wasu hamshakan ’yan kasuwa, wadanda suka gaya mini cewa hanyar da ake samun kudi da gaugawa ita ce mutum ya sadaukar da wata gaba ta jikinsa”.
Mujallar ta ruwaito cewa mutumin ya kai kansa dajin kasar Zambiya ne da misalin karfe hudu na yamma ranar Litinin din makon da ya gabata.
Ya ci gaba da cewa, “An umarce ni na yi tsirara, sai wata kura ta taho ta fara cin yatsun kafata daga bisani kuma ta cinye azzakarina da marenana. Kodayake bokana bai fayyace wane yanki na gabar jikina ne zan sadaukar ba, amma ina fatan zama hamshakin attajiri nan ba da dadewa ba. Ban damu da abin da ya same ni ba, ni dai burina na zama attajiri”.
Shi dai Zulu ya shafe kimanin watanni hudu yana kwadago a kasar Zambiya ba tare da samun biyan bukata ba.
Likitocin asibitin sun tabbatar da cewa Zulu yana murmurewa, bayan da ’yan sanda suka kawo shi asibitin cikin mawuyacin hali.