Ya bayar da tallar neman afuwar matarsa a motoci dubu da 407
Wani mazaunin birnin Yibin da ke gundumar Sichauan a kasar Sinya dauki hayar llunan talla da ake makala wa motocin tasi-tasi na birnin don kawai ya nemi afuwar matarsa. Mutanen wannan birnin sun yi matukar girgiza ganin kowace mota na dauke da tallar nenamn afuwa.Wannan talla dai na dauke da sakon da ke cewa: “Na […]
Wani mazaunin birnin Yibin da ke gundumar Sichauan a kasar Sinya dauki hayar llunan talla da ake makala wa motocin tasi-tasi na birnin don kawai ya nemi afuwar matarsa. Mutanen wannan birnin sun yi matukar girgiza ganin kowace mota na dauke da tallar nenamn afuwa.
Wannan talla dai na dauke da sakon da ke cewa: “Na tuba a yi hakuri masoyiyata. Ki yi mini afuwa.” An rubuta sunan wanda ya dauki nauyin wannan talla a matsayin A kiang. Kuma ya sa a baza wannan talla a daukacin allunan motocin tasi dubu da 407 da ke birnin Yibin, tun daga ranar Asabar zuwa Litinin.
Hotunan tasi din da ke dauke da tallace-tallacen ya bazu a shafukan intanet, inda masu mu’amkala a shafukan ke ta hasashen wane irin laifi mutumin ya yi wa matarsa na bacin rai.
Kamfanin da ke kula da tallace-tallace da ke kan allunan motocin tasin, na Huadi Metropolis Daily, ya bayyana cewa, sakonnin da aka buga a allunan motocin, na yi shi ne a kan kudi Yun dubu 10 (ko Dala dubu da 530), wato daidai da Naira Dubu 406 da 980 a kowace rana, sannan mutumin ya yi hayar allunan motocin na tsawon kwana uku.
Da wasu na tunanin ko shiri ne na kamfanimn tallace-tallace, amma sai kamfanin ya fito fili ya tabbatar wa al’umma cewa, talla ce ta hakika aka bayar. Kuma wanda ya san al’adar mutanen Sin wajen neman afuwar abokan zaman su na aure, ba zai yi mamaki ba.
Misalin neman afuwa a kasar Sin, sun hada da na Afrilun 2015, inda wani mutum ya taba sayen shafukan jaridrar BeijinYouth Daily har hudu don neman afuwar budurwarsa, ya kuma bar shafuka biyu, ba tare da ya rubuta komai ba. Sannan ya rubuta cewa: “Na kyale wadannan shafuka ne saboda ban san yadda zan ci gaba da rubutu ba.”
Sannan an sha baza hotunan magidantan da ke durkusawa don neman afu8war matansu ko matar aure ko budurwa a bainar jama’a, rowan sama na dukan su, kai har ma a shirin talabijin a kan nuna neman afuwa.