Ya bayyana dalilin da ya haddasa karuwar talauci a Najeriya

Wani kwararre a harkar ilimi, Dokta Elisha G. Kutara ya ce, watsi da gwamnatocin baya suka yi da harkar ilimin firamare ne musabbabin abin da ya janyo ake samun tazara tsakanin masu hannu da shuni da talakawa a kasar nan. Masanin, wanda tsohon Darakta ne a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, ya bayyana haka ne yayin […]

Ya bayyana dalilin da ya haddasa karuwar talauci a Najeriya
Ya bayyana dalilin da ya haddasa karuwar talauci a Najeriya

Wani kwararre a harkar ilimi, Dokta Elisha G. Kutara ya ce, watsi da gwamnatocin baya suka yi da harkar ilimin firamare ne musabbabin abin da ya janyo ake samun tazara tsakanin masu hannu da shuni da talakawa a kasar nan.

Masanin, wanda tsohon Darakta ne a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a Abuja. Ya ce: “Babu abin da muke gani a yanzu sai yadda ilimin firamare ya shiga halin-ni-’ya-su saboda watsin da gwamnati ta yi da shi. Babu makarantu, babu kayan aiki; wannan ya sanya an kara samun tazara. Masu kudi suna kai ’ya’yansu makarantun kudi sannan da sun kammala su kai su jami’o’in waje masu tsada.”
Ya bayyana cewa muddin aka ba ilimi kulawar da ta dace, hatta fakirai ma za su iya kai ’ya’yansu makaranta. Amma kamar yadda ya ce, gwamnati ba ta ba bangaren kulawar da ta dace. Saboda haka ne a ganinsa makarantun aka bar su suka lalace, babu malamai da kayan aiki.
Ya ce wannan shi ne babban dalilin da ya sa talakawa ba su tura ’ya’yansu makaranta a kasar nan. “Wannan shi ne babban abin da yake damunmu, musammam ma mu da muka yi makarantar gwamnati a shekarun baya a lokacin ilimi yana da daraja saboda kulawar da gwamnati take ba shi,” inji shi.
Saboda haka ya shawarci gwamnati mai ci da ta dauki matakan da suka dace don magance matsaloli da kalubalen da ke fuskantar ilimi. Ya bayyana cewa daya daga cikin matakan shi ne gwamnati ta sanya ido kan kudin da ta ware wa ilimi.
Ya bukaci gwamnati ta kafa kwamiti mai zaman kansa wanda zai rika bibiyar yadda ma’aikatu ke kashe kudin da gwamnati ta ba su. Ya ja hankalin ’yan majalisa su tashi tsaye wajen gudanar da ayyukan da suka rataya a kansu wajen ganin sun inganta ilimi a mazabunsu.