Ya bayyana yadda ya kashe ’yar shekara ta hanyar fyade
Matashin nan mai shekara 27 da ya shiga hannun ’yan sanda bisa zarginsa da laifin yi wa wata yarinya ’yar shekara biyu fyade har ta mutu a karamar Hukumar Sabon Garin Zariya, ta Jihar Kaduna yana hedkwatar ’yan sandan Kaduna inda ake ci gaba da bincike a kansa. A kwanakin baya Aminiya ta buga labarin […]
Matashin nan mai shekara 27 da ya shiga hannun ’yan sanda bisa zarginsa da laifin yi wa wata yarinya ’yar shekara biyu fyade har ta mutu a karamar Hukumar Sabon Garin Zariya, ta Jihar Kaduna yana hedkwatar ’yan sandan Kaduna inda ake ci gaba da bincike a kansa.
A kwanakin baya Aminiya ta buga labarin yadda matashin mai suna Shehu Bashiru ya yi fyade ga ’yar makwabcinsu mai shekara biyu har ta musu, inda bayan bincike aka samu gawarta a dakinsa. Wakilinmu ya samu labarin cewa an kai Shehu Bashir hedkwatar ’yan sandan ne a farkon watan Afrilu domin ci gaba da bincike kan lamarin.
Da yake karin bayani ga wakilinmu kan yadda lamarin ya auku, Shehu ya ce, “Gaskiya ban san abin da ya sa na aikata abin da ake zargina da shi ba, aikin Shaidan ne. Domin marigayiya Fatima ta shigo dakina ne saboda ’yar makwabtanmu ne kuma mun saba da ita.Tana shigowa sai na kwabe mata kaya na kama lalata da ita, abin mamaki sai na ga ta daina numfashi. Na yayyafa mata ruwa amma ba ta tashi ba daga nan ne na fahimci na shiga matsala.”
Wanda ake zargin ya kara da cewa: “Na kuma shiga damuwa ne lokacin da mahaifiyarta ta soma kiranta inda na fada mata ni ma ban ganta ba. Na harhada kayana da sunan zan kai su wanki amma ita ce a kudundune a ciki. Daga bisani babanta ya shigo dakina inda ya ce wai an fada masa cewa an ga ’yarsa ta shiga dakina sai na ce ya shigo ya bincika. Da ya shiga bai ga komai ba, har zai fita sai ya juyo ya bukaci in warware kayan wankin da ke gabana. A nan ne ya ga gawar ’yarsa nan take ya yi kuwwa inda mutane suka taru aka gayyato ’yan sanda suka zo.”
Mahaifin marigayiya Fatima, Malam Zakari dahiru cikin hawaye ya yi nadamar rashin ba ’yarsa Naira 50 ta sayi kosai, ya ce kila da ya ceci rayuwarta.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar DSP Abdullahi Zubairu ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce tuni an tura wanda ake zargi sashin binciken manyan laifuffuka domin ci gaba da bincike.