Ya binne gawar dansa bayan ya kashe shi kan zargin sata

Wani mutum mai suna Arogundade Ahmed, mai kimanin shekara 34 da ke zaune a unguwar Ikorodu a Legas ya kashe dansa, dan kimanin shekara 13 mai suna kudus da duka kan zargin yunkurin yi wa makwabtansa sata.Binciken Aminiya ya gano cewa bayan da Arogundade ya kashe dan nasa, a makon da ya gabata, sai ya […]

Ya binne gawar dansa bayan ya kashe shi kan zargin sata

????????????????????????????????????????????????????????????

Marigayi KudusWani mutum mai suna Arogundade Ahmed, mai kimanin shekara 34 da ke zaune a unguwar Ikorodu a Legas ya kashe dansa, dan kimanin shekara 13 mai suna kudus da duka kan zargin yunkurin yi wa makwabtansa sata.
Binciken Aminiya ya gano cewa bayan da Arogundade ya kashe dan nasa, a makon da ya gabata, sai ya haka kabari ya binne shi a kofar gidansa don kada mutane su gane.
Wata majiya ta bayyana cewa Arogundade ya fusata ne lokacin da mai gidan dansa da yake koya masa sana’ar kanikanci ya kawo masa karar cewa wata makwabciyarsa ta kawo karar dansa kudus cewa ya haura gidanta don ya yi mata sata.
Wani wanda lamarin ya faru  a kan idonsa, mai suna Adekoya, ya bayyana cewa lokacin da Arogundade ke dukan dansa babu wanda ya kai masa dauki saboda tsoron fushinsa da mutane ke yi. “Shi mutum ne mafadaci mai mutukar zuciya, kuma gaskiya makwabtansa na tsoronsa sosai. Shi ya sa lokacin da yake dukan yaron babu wanda ya kai dauki. Mun ji yana cewa sai ya kashe yaron tun da barawo yake so ya zama, kuma ga dukkan alamu ya yi amfani da adda ne ya rika dukansa da ita. Da ya ga ya mutu sai ya binne shi a kofar gida, mu kuma muka sanar da shugabanni, daga bisani suka sanar da ’yan sanda aka kama shi”. Inji shi.
Wani mai rike da sarautar gargajiya a yankin mai suna Oludapo Sule ya bayyana cewa lokacin da abin ya faru, ya sanar da ’yan sanda da kuma shugabannin kungiyar OPC.
Shi ma shugaban kungiyar mazauna yankin mai suna Mista Agboola Aluko ya ce Arogundade ya dade yana damun mutanen yankin. “Ya ma taba yi wa dansa mummunan rauni da adda a kan abin da bai kai ya kawo ba, kuma ya taba yin barazanar kashe duk wanda ya shiga al’amuransa”. Inji shi.
Bayanan ’yan sanda suka dauka ya nuna cewa Arogundade ya musanta zargin da ake yi masa na kisan dansa inda ya ce masu gidansa da ke koya masa sana’ar kanikanci Lateef da Gebriel su ne su ka kashe shi, a sakamakon azabtarwar da suka yi masa, don ya mutu ne jim kadan da kawo shi gida.
Lateef da Gebriel sun musanta zargin, suka ce kawai dai sun daure kudus a jikin wata bishiya, amma ba su kashe shi ba.
Mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Legas Ngozi Braide ta tabbatar da aukuwar lamarin.