Ya bukaci a kawo karshen yajin ma’aikatan shari’a a Jihar Yobe
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya reshen Jihar Yobe Malam Zakari Adamu ya zargi gwamnatin jihar kan yin sakaci dangane da yajin aikin da ma’aikatan kula da shari’a na jihar ke yi a tsawon lokaci. Shugaban ya ce, yajin aiki da ma’aikatan shari’a ke yi a jihar ya yi matukar jefa mutanen da ke jiran a […]
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya reshen Jihar Yobe Malam Zakari Adamu ya zargi gwamnatin jihar kan yin sakaci dangane da yajin aikin da ma’aikatan kula da shari’a na jihar ke yi a tsawon lokaci.
Shugaban ya ce, yajin aiki da ma’aikatan shari’a ke yi a jihar ya yi matukar jefa mutanen da ke jiran a yi musu shari’a cikin mummunan hali domin da yawa daga cikinsu na samun kansu cikin kamuwa da cututtukan da kan kai su ga rasa rayukansu ba tare da samun kula ba.
Ya kara da cewa hali da tsararrun da ke jiran shari’a ke ciki babu wanda ya haddasa musu in ba gwamnatin jihar ta Yobe ba domin kuwa inda a ce gwamnatin ta san hakkin jama’a da tuni ta sasanta da ma’aikatan shari’ar don su koma bakin aikinsu.
Malam Zakari Adamu ya ce duk wanda ya dubi halin da mutanen da ke rufe a ofisoshin ’yan sanda suna jira a kai su kotu amma hakan ya faskara ke ciki duk da cewa dokar kasa ta ce kada a bar mutum a wurin ’yan sanda ya wuce awa 24, to, lallai zai tausaya musu.
Saboda haka ya nemi gwamnatin Jihar Yobe da ta nemi zaman gaggawa da ma’aikatan shari’ar don sasantawa su koma aiki tunda yake yajin aikin da suka yi duk na kasa ne amma daga bisani wasu gwamnatocin jihohi sun shirya da mutanensu sun koma ga aiki.