Ya bukaci al’ummar Gombe su saka wa dankwambo
Wani tsohon Babban Sakatare a Gwamnatin Tarayya kuma Kwamsihinan Lafiya na farko a Jihar Gombe Dokta Ibrahim Jalo Daudu, ya bukaci al’ummar jihar su saka wa Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo ta wajen sake zabensa a bana. Dokta Ibrahim Jalo ya yi wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Gombe, […]
Wani tsohon Babban Sakatare a Gwamnatin Tarayya kuma Kwamsihinan Lafiya na farko a Jihar Gombe Dokta Ibrahim Jalo Daudu, ya bukaci al’ummar jihar su saka wa Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo ta wajen sake zabensa a bana.
Dokta Ibrahim Jalo ya yi wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Gombe, inda ya ce babu abin da jama’ar jihar za su yi su saka wa Gwamna Ibrahim dankwambo game da ayyukan raya kasa da ya samar a jihar sai sake zabensa a karo na biyu a zaben da za a gudanar a watan Maris mai zuwa.
Dokta Jalo ya ce idan jama’ar Jihar Gombe suka sake bai wa dankwambo dama karo na biyu zai sake gina jihar ta hanyar samar da hanyoyin dogaro da kanta maimakon dogaro da kudin man fetur.
Ya ce tun kirkiro jihar shekara 19 da suka wuce ba a samu ci gaban da aka samu irin na shekara hudu na Gwamna dankwambo ba, “Domin duk wanda ya zo Gombe cikin wadannan shekaru zai ga an samu ci gaba sosai,” inji shi.
Dokta Daudu, ya jinjina wa Gwamna dankwambo kan yadda ya farfado da martabar matasa sama da dubu uku ya mai da su mutane a bangarorin rayuwa daban-daban da ake kiran su Marshal. Dokta Jalo ya yi kira ga jama’ar jihar su kauce wa siyasar gaba su gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali ba tare da tada hatsaniya ba.