Ya bukaci Buhari ya farfado da kananan masana’antu

Shugaban Jam’iyyar NDP reshen Jihar Bauchi Malam Abubakar dandada ya bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya farfado da kananan masana’antun da suka kwanta dama.Malam Abubakar dandada wanda har wa yau shi ne Babban Sakataren kungiyar Mahauta ta kasa ya kara da cewa a madadin Majalisar Sarakunan Fawa ta Najeriya suna rokon Shugaban kasa Muhammadu Buhari […]

Ya bukaci Buhari ya farfado da kananan masana’antu
Ya bukaci Buhari ya farfado da kananan masana’antu

Shugaban Jam’iyyar NDP reshen Jihar Bauchi Malam Abubakar dandada ya bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya farfado da kananan masana’antun da suka kwanta dama.
Malam Abubakar dandada wanda har wa yau shi ne Babban Sakataren kungiyar Mahauta ta kasa ya kara da cewa a madadin Majalisar Sarakunan Fawa ta Najeriya suna rokon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya farfado da kananan masana’antu domin hakan zai magance matsaloli da dama da suka hada da na tsaro da rashin aikin yi.  “Ina tabbatar wa al’umma cewa idan aka farfado da kananan masana’antun da suka kwanta dama, to za a rage sama da kashi 85 cikin 100 na matsalolin matasan Najeriya, domin hakan zai taimakawa wajen samar wa matasa aikin yi, kowa ya san cewa idan aka samar wa matasa aiki, to, tabbas za a samu karancin barayi da masu aikata miyagun laifuffuka a tsakanin al’umma,” inji shi.
Alhaji dandada ya yi kira ga iyayen yara su rika sanya ido sosai kan tarbiyyar ’ya’yansu domin kowa zai amsa tambaya ranar gobe kiyama a gaban Allah kan kiwon da Ya ba shi.
“Kuma a matsayinmu na shugabannin kungiyar mahauta ta kasa za mu ci gaba da yin addu’a ga gwamnatin Muhammadu Buhari domin tana da manufofi masu kyau na bunkasa rayuwar ’yan Najeriya,” inji shi.