Ya bukaci gwamnati ta kafa Hukumar Kula da Makarantun Islamiyya

Shugaban kungiyar Makarantun Islamiyya reshen Jihar Filato (Ittihadu AnwarilHidayat) Alhaji Yusuf Yahaya ya bukaci Majalisar Dokoki ta kasa ta kafa wata doka da za ta  kafa Hukumar Kula da Makarantun Islamiyya ta kasa. Alhaji Yusuf Yahaya ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu A Jos, inda ya ce akwai dubban […]

Ya bukaci gwamnati ta kafa Hukumar Kula da Makarantun Islamiyya
Ya bukaci gwamnati ta kafa Hukumar Kula da Makarantun Islamiyya

Shugaban kungiyar Makarantun Islamiyya reshen Jihar Filato (Ittihadu Anwaril
Hidayat) Alhaji Yusuf Yahaya ya bukaci Majalisar Dokoki ta kasa ta kafa wata doka da za ta  kafa Hukumar Kula da Makarantun Islamiyya ta kasa.
Alhaji Yusuf Yahaya ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu A Jos, inda ya ce akwai dubban makarantun Islamiyya a kasar nan tare da miliyoyin
dalibai, kuma makarantun suna da tsarin karatun firamare da sakandire har da jami’a.
“Amma abin takaici gwamnatocin jihohi da dama ba su damu da makarantun ba, balle su san yadda suke gudanar da harkokinsu,” inji shi.
Ya ce makarantun Islamiyya na da matukar tasiri a Najeriya da duniya domin manyan malaman kasar nan makarantun suka yi.
Alhaji Yusuf Yahaya ya ce hatta kungiyar Jama’atu Nasril Islam ba ta san yadda makarantun Islamiyya na kasar nan suke tafiyar da harkokinsu ba.
Ya bukaci manyan kungiyoyin addinin Musulunci na kasar nan su hada kai don ganin an kafa hukuma ta kula da makarantun Islamiyya, saboda taimakon da hakan zai yi ga makarantun Islamiyya a kasar nan.