Ya bukaci gwamnati ta kara ba da goyon baya kan yaki da miyagun kwayoyi
Shugaban Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun kwayoyi (NDLEA) a yankin Akwanga da ke Jihar Nasarawa, Malam Sa’idu Salisu Mungadi ya bukaci gwamnatin jihar ta kara bayar da goyon baya wajen yaki da miyagun kwayoyi a tsakanin matasa don samar da al’umma mai kyakkyawar makoma. Malam Sa’idu Mungadi ya bayyana haka ne a lokacin da yake […]
Shugaban Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun kwayoyi (NDLEA) a yankin Akwanga da ke Jihar Nasarawa, Malam Sa’idu Salisu Mungadi ya bukaci gwamnatin jihar ta kara bayar da goyon baya wajen yaki da miyagun kwayoyi a tsakanin matasa don samar da al’umma mai kyakkyawar makoma.
Malam Sa’idu Mungadi ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a ofishinsa, inda y ace a cikin shekara fiye da 20 da kafuwar hukumar ta tashi haikan wajen yakar masu sha ko safara ko fataucin miyagun kwayoyi da tabar wiwi da hodar Iblis a kasar nan.
Ya ce ba aikin hukumar ne ta ci tarar wanda aka kama da miyagun kwayoyi ba, aikinta shi ne ta mika shi ga kotu ko kuma shirya tarurrukan fadakar da jama’a kan illar tu’ammali da miyagun kwayoyin tare da tsare wadanda miyagun kwayoyin suka yi wa illa a gidajen gyara hali, don ba su shawarwari ta yadda za su yi watsi da haka.
“Kodayake a duk wani aiki akwai batagari a iya sanina babu wata tara da aka yarda jami’in hukumar nan ya yi wa wanda ake zargi da laifi. Namu horarwar ce da ba da shawarwari, idan kuma laifin nasu ya yi yawa, sai mu kai su kotu domin yi musu hukuncin da ya dace,” inji shugaban.
Malam Sa’idu Mungadi ya shawarci matasan Najeriya su guje wa shaye-shaye domin tsira da mutuncinsu da lafiyarsu, inda ya ce babu irin matsalar da shaye-shaye ba sa kawo wa dan Adam a duniya, saboda duk wani mugun abu da mutun zai yi sai ya yi shaye-shaye, kamar sata da fyade da kisan gilla, har ma ’yan Boko Haram duk suna yin aika-aikarsu ne sakamakon shaye-shaye.