Ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta inganta makarantun Tsangaya

Shugaban Kwamitin Kula da Makarantar Tsangaya ta garin dan’alhaji a karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna Malam Yusuf Rabi’u dan’alhaji ya bukaci Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohin arewacin kasar nan, su inganta makarantu Tsangaya don samar da ingantaccen ilimin addini.  Malam Yusuf Rabi’u dan’alhaji ya bukaci haka ne a lokacin da yake zantawa dawakilinmu, […]

Ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta inganta makarantun Tsangaya
Ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta inganta makarantun Tsangaya

Shugaban Kwamitin Kula da Makarantar Tsangaya ta garin dan’alhaji a karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna Malam Yusuf Rabi’u dan’alhaji ya bukaci Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohin arewacin kasar nan, su inganta makarantu Tsangaya don samar da ingantaccen ilimin addini. 

Malam Yusuf Rabi’u dan’alhaji ya bukaci haka ne a lokacin da yake zantawa da
wakilinmu, inda ya ce babu rike tsarin makarantun Tsangaya tare da inganta su zai dada taimaka wa wajen kauda da yara masu barace-barace a kan titunan kasar nan.
Malam Yusuf Rabi’u ya ce makarantun Tsangaya sun samu nasarar killace yaran da suke yawo a tituna da gidaje suna barace-barace tare koyar da daliban karatun Alkur’ani da na boko.
Ya ce “A yanzu daliban da suke karatu a makarantun Tsangaya sun fi daliban da suke karatu a makarantun boko na gwamnati karatun boko. Don haka muna kira ga sabuwar gwamnatin nan ta sanya ido kan wadannan makarantu ta tallafa musu. Domin wadannan makarantu za su ci gaba da magance barace-baracen da kananan yara ke yi a kan tituna, tare da samar da yara masu tarbiyya da za su taimaka wajen kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.”
Ya ce duk da nasarorin da makarantun suka samu akwai matsaloli da dama da suke fuskanta da suka hada da rashin tsara biyan malaman da suke koyar da karatun Alkur’ani da rashin samar da isasshen abinci ga daliban makarantun.