Ya bukaci gwamnatoci su taimaka wa fataken shanu

Shugaban Fataken Shanu, rashen Jihar Edo, Alhaji Sani Musa Kwajole ya yi kira tare da rokon gwamnatocin kasar nan su taimaka wa fatake masu sana’ar  sayar da dabbobi, musamman wajen ba su rancen kudi saboda su samu damar bunkasa sana’ar tasu, wadda ke taimaka wa al’umman kasa gaba daya.Alhaji Sani ya yi wannan kiran tare […]

Ya bukaci gwamnatoci su taimaka wa fataken shanu

Shugaban Fataken Shanu, rashen Jihar Edo, Alhaji Sani Musa KwajoleShugaban Fataken Shanu, rashen Jihar Edo, Alhaji Sani Musa Kwajole ya yi kira tare da rokon gwamnatocin kasar nan su taimaka wa fatake masu sana’ar  sayar da dabbobi, musamman wajen ba su rancen kudi saboda su samu damar bunkasa sana’ar tasu, wadda ke taimaka wa al’umman kasa gaba daya.
Alhaji Sani ya yi wannan kiran tare da bayyana bukatar kungiyar fataken a wata hira da Aminiya a wannan makon. “Mun ji cewa akwai wani shiri da gwamnatin kasar nan ta yi inda ta ware wani kudi na musamman domin tallafa wa ’yan kasuwa da sauran masu sana’a a kasar nan. Mu a kungiyarmu muna kira da rokon wannan shirin ya kawo gare mu ta yadda za mu kara bunkasa sana’armu”.
Daga nan kuma sai Alhaji Kwajole ya shawarci ’ya’yan kungiyar fataken, musamman na reshen jihar da kuma na kasa baki daya da su goya wa shugabanninsu baya da ba su hadin kai kan abin da ya shafi harkar wannan sana’ar.   Kuma ya yi kira ga shugabannin kungiyar da su rika tuntubar juna a kowane lokaci domin samun fahimta dangane da inda aka sa gaba.
A karshe Alhaji Sani ya gode wa Gwamna Adams Aliu Oshiomhole a kan kaunar da yake yi wa ’yan Arewa mazauna jihar ya kuma yaba da ayyukan da gwamnan yake ci gaba da aiwatarwa a cikin jihar domin ci gaban al’umma.