Ya bukaci gwamnatocin jihohin Kudu su samar wa makiyaya burtaloli

An bukaci gwamnatocin jihohin Kudu su taimaka su samar wa al’ummar Fulani makiyaya burtaloli da mashayar dabbobi da wuraren kiwo, lamarin da zai taimaka matuka wajen saukaka irin matsalolin da suke fama da su a yankunan.Alhaji Shu’aibu Haruna Sogiji, wanda shi ne shugaban kungiyar matasan Fulani makiyaya (ANFON) ya yi wannan kiran a wata tattaunawa […]

Ya bukaci gwamnatocin jihohin Kudu su samar wa makiyaya burtaloli
Ya bukaci gwamnatocin jihohin Kudu su samar wa makiyaya burtaloli

An bukaci gwamnatocin jihohin Kudu su taimaka su samar wa al’ummar Fulani makiyaya burtaloli da mashayar dabbobi da wuraren kiwo, lamarin da zai taimaka matuka wajen saukaka irin matsalolin da suke fama da su a yankunan.
Alhaji Shu’aibu Haruna Sogiji, wanda shi ne shugaban kungiyar matasan Fulani makiyaya (ANFON) ya yi wannan kiran a wata tattaunawa da wakilin Aminya a ziyararsa da ya yada zango a garin Benin kwanan baya.
Ya ce idan aka duba gaba daya an rigaya an kange kusan ko’ina, inda ya ba da misali da yankin dajin Akpilla da Jattu har  Auchi zuwa Abiele da Iguebe da Igbonki har  ya fada  Uronigbe, “Babu wurin da mai kiwo zai sake da dabbobinsa, ya samu natsuwar kiwonsu.
Ya ce idan aka samar da wadannan wurare da sinadaran kiwo za a magance da yawa daga cikin tashin-tashinar da akan samu tsakanin makiyaya da manoma.  
A karshe ya yi fatar gwam-natocin za su taimaka wajen jin wannan kuka kuma su yi tsayin daka wajen ganin sun tabbatar da samuwar wadannan abubuwa da kuma aiwatar da su.
Sai dai kuma mai magana da yawun kungiyar manoma a Jihar Edo, Mista Emma, yayin da yake tofa albarkacin bakinsa dangane da lamarin da ke tsakaninsu da makiyaya, ya ce babbar matsalarsu ita ce barna da ganganci ba batun rashin makiwata ko mashayar dabbobi ba.  
“Farkon shigarsu yanku-nanmu, mun dauke su tamkar ’yan uwa, muna barin suna shiga ko’ina, amma sai suka bullo da wata mugunta ta yi mana barna da ganganci”.  Inji shi.