Ya bukaci jama’a su yi addu’a ga shugabanni

Sheikh Nasir Abdulmuhiya ya bukaci jama’a su ci gaba da yin addu’o’i na musamman ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Bauchi Barista Mohammed Abubakar da sauran shugabanni domin babu abin da suke bukata kamar addu’a da goyon baya. Sheikh Nasir Abdulmuhi ya bayyana haka a lokacin bude tafsiri a masallacin Juma’a na Bakin […]

Ya bukaci jama’a su yi addu’a ga shugabanni
Ya bukaci jama’a su yi addu’a ga shugabanni

Sheikh Nasir Abdulmuhiya ya bukaci jama’a su ci gaba da yin addu’o’i na musamman ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Bauchi Barista Mohammed Abubakar da sauran shugabanni domin babu abin da suke bukata kamar addu’a da goyon baya.

Sheikh Nasir Abdulmuhi ya bayyana haka a lokacin bude tafsiri a masallacin Juma’a na Bakin Kura da ke Bauchi, bayan da kungiyar Izala ta kasa ta sake tura shi don gabatar da tafsiri bana.
Ya yaba wa Gwamna Mohammed Abubakar kan yadda ya dauki nauyin sa tafsirin kungiyar a gidan rediyon Jihar Bauchi (BRC) da gidan talabijin na BATb.
Da yake tofa albarkacin bakinsa a wurin bude tafsirin Babban Limamin Masallacin Juma’a na Gwallaga, Imam Ibrahim Idris ya shawarci al’ummar Musulmi su yi amfani da darussan da za su koya a cikin watan azumin Ramadan.
Honarabul Shu’aibu Isma’il Rahama ne ya wakilci Gwamnan a wurin taron kuma ya ce Gwamnan ya je da kansa amma saboda dalilai na aiki yana fatar alheri ga kungiyar kuma kofarsa a bude take domin bada gudunmawa wajen ciyar da Musulunci gaba.
Daga bisani malamin ya mika godiya ga Farfesa Suleiman Abdullahi da Alhaji Garba Muhammed Noma da Alhaji Shehu Aliyu Barden Gabas da Honarabul Abdulrazak Nuhu Zaki da Alhaji Usman mai kamfanin motoci na Usmaniyya da mutanen da suke bada gudunmawa ga kungiyar.