Ya bukaci magoya bayan APC a Jihar Oyo su mara wa gwamnati
Mataimakin Shugaban Kwamitin Al’ummar ’yan Arewa magoya bayan jam’iyar APC a Jihar Oyo, Alhaji Yahya Dauda, ya ce harsashin ginin zama lafiya da kwanciyar hankali da Gwamna Abiola Ajimobi ya dora tun farkon mulkinsa, shi ne babban dalilin da ya sa suka bar kowace jam’iyya suka rungumi ta APC a Jihar Oyo.Alhaji Yahya, wanda ya […]

Mataimakin Shugaban Kwamitin Al’ummar ’yan Arewa magoya bayan jam’iyar APC a Jihar Oyo, Alhaji Yahya Dauda, ya ce harsashin ginin zama lafiya da kwanciyar hankali da Gwamna Abiola Ajimobi ya dora tun farkon mulkinsa, shi ne babban dalilin da ya sa suka bar kowace jam’iyya suka rungumi ta APC a Jihar Oyo.
Alhaji Yahya, wanda ya fadi haka cikin hirarsu da Aminiya, ya ce, “a baya, mutanenmu sun rika shiga kunci, musamman a cikin kasuwanni da wuraren sana’o’i ta yadda wasu ’yan dabar siyasa suka hana su sakat, “Suna wasoson kayanmu har da kashe mutanenmu, amma a yanzu Gwamna Abiola Ajimobi ya yi maganin irin wannan varna, saboda haka muna goyon bayan wannan tafiya har zuwa zaven shekara ta 2015.”
A game da irin ci gaban da aka samu a Jihar Oyo, Alhaji Yahya ya ce, “Mutumin da ya yi shekaru 3 rabonsa da birnin Ibadan, idan ya shigo garin yanzu zai yi mamaki, musamman saboda irin ayyukan ci gaba kamar hanyoyi da ake ginawa da kawata garin, sannan an vullo da shirin samar da ayyuka ga matasa. Wannan al’amari kuwa ya hade a sauran garuruwan jihar, wanda gwamnatocin baya suka kasa yi a lokacinsu”.
A kan irin dari-darin shiga cikin jam’iyar da ke mulki a jihohin Yamma da wasu ’yan Arewa ke yi, Alhaji Yahya ya ja hankalinsu da su saki jiki don a samu kaiwa ga ci gaba. Ya ba da misali da wasu gwamnatocin jihohin Arewa da suka janyo kabilun Yarabawa da Ibo suka tsoma su a cikin harkokin mulki suna tafiya tare da su, lamarin da ba haka yake a wannan sashe ba, “Saboda mun ki fitowa mu hada kanmu domin a tafi tare damu, ya kamata mu dawo daga rakiyar madoki kusa maceci nesa”. Inji shi.
Ya ce, “Wani karin haske shi ne a ranar lahadi da ta wuce ne kungiyar Miyetti Allah ta Jihar Oyo, ta kawo mana ziyara a babban ofishinmu dake unguwar Sabo Ibadan, a inda Shugaban kungiyar ya nemi mu taimaka musu wajen ganin sun kusanci mahukunta a Jihar Oyo domin samo hanyar kawo karshen matsalolinsu. Ka ga wannan abun farin ciki ne da mutanenmu suka fara gane kura-kuran da suka yi a baya domin yin gyara a yanzu. Kuma, mun tabbatar musu cewa, za mu isar da kukansu ga gwamnatin jam’ijyar APC da Gwamna Ajimobi yake rike da ragamarta, musamman da yake akwai matukar bukatar wadannan mutane idan zaven shekara ta 2015 ya iso.”