Ya bukaci makiyaya da manoma su zauna lafiya
Shugaban Al’ummar Arewa mazauna garin Benin a Jihar Edo, Alhaji Badamasi Saleh ya shawarci Fulani makiyaya na jihar su sanya tsoron Allah a zukatansu da bin doka da oda dangane da kiwon dabbobinsu.Alhaji Badamasi ya bayar da shawarar ce a wata hira da ya yi da jaridar Aminiya, inda ya nuna cewa bin wannan shawara […]
Shugaban Al’ummar Arewa mazauna garin Benin a Jihar Edo, Alhaji Badamasi Saleh ya shawarci Fulani makiyaya na jihar su sanya tsoron Allah a zukatansu da bin doka da oda dangane da kiwon dabbobinsu.
Alhaji Badamasi ya bayar da shawarar ce a wata hira da ya yi da jaridar Aminiya, inda ya nuna cewa bin wannan shawara zai taimaka wajen samar da tabbatacen zaman lafiya a tsakaninsu da manoman jihar.
Ya ce abin da yake ci gaba da faruwa tsakanin makiyaya da manoma a wannan jihar, babbar matsala ce wadda ta kamata duk mai hankali ya damu da ita. “Tunda ciyawa ce cimar dabbobi ba masara da rogo da doya da kankana da sauran amfanin gona ba, kuma alhamdulillahi, muna da ita wadatatta a nan sashen, akwai bukatar kowanen wadannan bangarori su kiyaye hakkokin junansu”. Inji shi.
Ya bukaci bangarorin biyu su taimaka wajen sassauta al’amurran da ka tashi a tsakaninsu, musamman wajen guje wa daukar doka a hannunsu, tunda yake akwai hukuma wadda da dadewa ta kira taron sulhu. “Muna fata a rika duba da tuna irin taron sulhun da wani kwamishinan ’yan sanda na jihar ya taba kira na a rika yin taka-tsantsan da kuma girmama juna wajen kyautata mu’amala tsakanin juna”.
A karshe ya bukaci shugabannin kowane sashe na manoman da makiyayan su kara kaimi wajen ya wa mutanensu kunne wajen kokarin bin doka da oda don a sami zaman lafiya mai dorewa a tsakaninsu.