Ya bukaci matasa su ba da gudunmawa kan tsaro a kasar nan

Shugaban Kwamitin Wa’azin Matasa na kasa na kungiyar Jama’atu IzalatilBidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Ustaz Muhammad Murtala Idris Malwaya bukaci matasan kasar nan, su ci gaba da bada gudunmawa kan harkokin tsaro a kasar nan, domin ganin an kare rayuka da dukiyoyin al’umma daga hare-haren miyagu.Ustaz Muhammad Murtala Idris Malwa ya yi wannan kira […]

Ya bukaci matasa su ba da gudunmawa kan tsaro a kasar nan
Ya bukaci matasa su ba da gudunmawa kan tsaro a kasar nan

Shugaban Kwamitin Wa’azin Matasa na kasa na kungiyar Jama’atu Izalatil
Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Ustaz Muhammad Murtala Idris Malwa
ya bukaci matasan kasar nan, su ci gaba da bada gudunmawa kan harkokin tsaro a kasar nan, domin ganin an kare rayuka da dukiyoyin al’umma daga hare-haren miyagu.
Ustaz Muhammad Murtala Idris Malwa ya yi wannan kira ne a lokacin da
yake jawabi a wajen rufe taron bita da kwamitin ya shirya a garin Jos.
Ya ce “Mu tashi mu kara zage damtse wajen ba da gudunmawarmu ga harkokin  tsaro a kasar nan, hakan ya zama wajibi saboda yadda miyagu suka fantsama a ko’ina a kasar nan suna cutar da al’umma.”
Ustaza Malwa ya ce matasa su kara tsaurara matakan tsaro tare da sanya ido a gidaje da wuraren ibada da kasuwanni da tashoshin mota da asibitoci da makarantu dare da rana.
Ustaz Muhammad Murtala ya ce a watan Ramadan da ya gabata kwamitin, ya ziyarci
gidan yarin Jos inda ya tallafa wa fursunoni da kayan abinci tare da gyara masallacin gidan yarin. Har ila yau ya ce sun ziyarci asibitoci tare da tallafa wa marasa lafiya.
A makalar da ya gabatar a wajen taron, mai taken “Muhimmmancin Sana’a,” Sakataren ’Yan Agaji na kasa na kungiyar, Ustaz Muhammad Abubakar ya ce rashin sana’a ko aikin yi kan lalata tunani da kashe zuciya da rashin kishi da zubar da mutunci da saba wa Ubangiji. Don haka ya yi kira ga matasa su tashi su rungumi sana’o’i tare da inganta sana’o’in da suke yi.