Ya bukaci matasa su daina bari ana amfani da su wajen tada hankali
Shugaban matasan yankin Kebbi ta Kudu Alhaji Junaidu dahiru Wasagu ya bukaci matasan kasar nan, musamman na Arewa su daina bari batagarin ’yan siyasa suna amfani da su wajen tayar da hankali, musamman a lokutan yakin neman zabe ko jefa kuri’a, musamman a wannan lokaci da babban zaben 2015 ke karatowa. Alhaji Junaidu dahiru Wasagu […]
Shugaban matasan yankin Kebbi ta Kudu Alhaji Junaidu dahiru Wasagu ya bukaci matasan kasar nan, musamman na Arewa su daina bari batagarin ’yan siyasa suna amfani da su wajen tayar da hankali, musamman a lokutan yakin neman zabe ko jefa kuri’a, musamman a wannan lokaci da babban zaben 2015 ke karatowa.
Alhaji Junaidu dahiru Wasagu ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi, inda ya cewa kiran ya zama wajibi bisa la’akari da yadda kasar nan, musamman yankin Arewa yake komawa baya.
Shugaban ya bukaci matasan su rika kalubalantar duk dan siyasar da ya umarce su da yin bangar siyasa, kan su jera tare da shi a yayin tayar da zaune-tsayen.
Alhaji Junaidu Wasagu ya nuna rashin amincewarsa da dalilan da wasu ke bayarwa cewa talauci ne ke jefa matasan cikin wannan halin, inda ya ce idan talauci ne nawa ake ba matasan, kuma abin da ake ba su ya magance musu talaucin?
Ya tunatar da matasan cewa, za su iya kaiwa ga duk wani matsayi a kasar nan, saboda haka kada su watsar da damar da Allah Ya ba su, domin samun ’yar karamar biyan bukata mai wucewa.
Alhaji Junaidu Wasagu ya koka kan da yadda rayuwar matasan Arewa take shiga wani hali na koma baya, idan aka kwatanta su da takwarorinsu da ke sauran shiyyoyin kasar nan, saboda haka sai ya bukaci su mike tsaye wajen neman na kansu ba tare da dogaro da gwamnati ko ’yan siyasa ba.