Ya bukaci Musulmi su yi himma don cin gajiyar falalar Ramadan
Tsohon Limamin Sojoji Malam Abubakar Atiku, Walin Kalgo ya nemi Musulmi, su tashi tsaye su nemi falalar da ke cikin watan Ramadan ta hanyar kyautata mu’amala tsakaninsu da kuma yawaita karatun Alkur’ani da yin sauran ayyukan alheri. Malam Abubakar Atiku ya ce bai kamata Musulmi ya zauna hira mara amfani ba tare da yin aikin […]
Tsohon Limamin Sojoji Malam Abubakar Atiku, Walin Kalgo ya nemi Musulmi, su tashi tsaye su nemi falalar da ke cikin watan Ramadan ta hanyar kyautata mu’amala tsakaninsu da kuma yawaita karatun Alkur’ani da yin sauran ayyukan alheri.
Malam Abubakar Atiku ya ce bai kamata Musulmi ya zauna hira mara amfani ba tare da yin aikin lada da zai sada shi da samun rahamar Allah cikin wannan wata ba.
Shehin Malamin ya ce kuma ya zama wajibi Musulmi su kaurace wa manya da kananan laifuffuka kuma su yawaita tuba zuwa ga Allah, domin Manzon Allah (SAW), ya ce shi kansa a duk rana yana tuba ga Allah sau saba’in “Don haka wajibi ne mu Musulmi mu yi koyi mu rika yawan tuba zuwa ga mahaliccinmu koyaushe,” inji shi.
Limamin ya kara da cewa, a cikin wannan wata akwai falala da garabasa na samun lada, “Akwai wata kofa a gidan Aljanna mai suna Rayyan babu wanda zai shige ta cikinta sai masu yin azumi, don haka ina kwadaitar da Musulmi mu dage mu nemi zama wadanda za su bi ta cikin wannan kofa,” inji shi.
Sai ya roki Allah, Ya kara hada kan Musulmi, musamman a wannan lokaci da suke fama da tsangwama a duniya, kuma rashin hadin kai da rarrabuwa da son zuciyar wasunsu ne yake haifar da haka.