Ya bukaci Musulmi su yi wa Najeriya addu’a

Kansila mai wakiltar mazabar Kubwa a yankin Bwari da ke Birnin Tarayya, Abuja, Malam Aliyu Salihu na Jam’iyyar APC ya bukaci al’ummar Musulmi su dauki watan azumin Ramadan a matsayin watan rahama da jinkai tare da yin amfani da shi wajen yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Najeriya addu’o’in alheri, domin ci gaban […]

Ya bukaci Musulmi su yi wa Najeriya addu’a
Ya bukaci Musulmi su yi wa Najeriya addu’a

Kansila mai wakiltar mazabar Kubwa a yankin Bwari da ke Birnin Tarayya, Abuja, Malam Aliyu Salihu na Jam’iyyar APC ya bukaci al’ummar Musulmi su dauki watan azumin Ramadan a matsayin watan rahama da jinkai tare da yin amfani da shi wajen yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Najeriya addu’o’in alheri, domin ci gaban kasar nan da dorewarta.
Honorabul Aliyu Salihu ya ce, salon shugabancin Shugaba Buhari, zai kai Najeriya ga tudun mun-tsira wajen bunkasar tattalin arziki da samar da aikin yi, inda ya ce manufar gwamnatin APC ta Shugaba Buhari ba ya tsaya kan yaki da cin hanci ne kadai ba, har ma zai rage talauci tare da bunkasa nomad a samar da zaman lafiya don amfanin talakawa. Sai ya yi fatan al’ummar Musulmi za su dabbaka kyawawan darussan da azumin yake koyarwa, inda ya gode wa Allah kan yadda Ya ba Najeriya Shugaban kasa nagari da yake da zimmar kyautata makomar Najeriya.